Barkanmu da warhaka, a yau na kawo muku yadda ake girki mai suna Gas meat.
Ana sayar da wannan gasasshen nama kusan ko’ina. Amma ba a san yadda ake sarrafa shi ba.
Ya kamata a yi wa maigida irin wannan gashi domin sanya kunnensa motsi.
– Kayan hadi
- Naman rago (ba mai kitse ba)
- Albasa 5
- Garin kuli-kuli
- Garin citta
- Man gyada
- Gishiri
- Magi
- Curry
- Thyme
– Yadda ake hadin
Bayan an wanke nama sai a yanka shi sala-sala, a yanka albasa ita ma sala-sala.
A dora naman a tukunyar da ake suyar kosai, sai a rufe a jira na tsawon minti 20.
Bayan naman ya nuna da ruwan jikinsa, sai a fara gauraya shi da cokalin girki.
Sannan a zuba yankakkiyar albasa da dakakken kuli-kuli da man gyada da dakakkiyar citta da curry da thyme da gishiri kadan da magi daidai dandanon da ake so.
Sai a yi ta gaurayawa har sai albasar ta nuna, sai a sauke.