✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka tuwon shinkafa miyar ganyen Ugwu

Barkanmu da sake saduwa da iayaen gida tare da fatan alheri kuma ana lafiya. Kamar yadda nake ba da shawarwari a kullum cewa yana da…

Barkanmu da sake saduwa da iayaen gida tare da fatan alheri kuma ana lafiya. Kamar yadda nake ba da shawarwari a kullum cewa yana da kyau mace ta koyi girki daban-daban musamman idan maigida ya kasance mai yawan son cin tuwo, to ya zama wajibi a kan mace ta koyi girka miya daban-daban ga maigida. Idan ba ta koya ba, za a kawo mata wadda za ta zo ta koya mata wato abokiyar zama.

Kayan hadi

Tuwon shinkafa

•   Shinkafar tuwo

•   Ruwa

Hadi

A jika shinkafar tuwo a ruwa ta jika kamar na awa daya. Sai a dora ruwa a wuta bayan ya tafasa sai a wanke jikakkiyar shinkafar a zuba sannan a rage wuta a rufe da marufin tukunya. Bayan minti 20 zuwa 25 sai a sauke a tuka. A kwashe a leda sannan a ajiye a kwano wa maigida.

 

Miyar ganyen Ugwu

Abubuwan da za a bukata

•         Ganyen Ugwu

•         Ganda

•         Kifi banda

•         Albasa

•         Tumatir

•         Attarugu

•         Magi

•         Kori

•         Manja

•         Garin tafarnuwa

Hadi

A wanke ganda da ruwan zafi sannan a sanya  a tukunyar dafa ganda a yanka albasa kadan da gishiri sai a rufe a dora a wuta. Bayan minti 40 sai a sauke a ajiye a gefe. A wanke ganyen Ugwun da gishiri da ruwa sannan a yayyanka a ajiye a gefe. A wanke kifi banda da ruwan zafi sannan a gutsura shi kanana a ajiye a gefe.

A dora tukunya a wuta sannan a zuba manja bayan ya yi zafi, sai  a zuba yankakkiyar albasa da tumatir da jajjagen attarugu a yi ta soyawa har su soyu. Bayan sun soyu, sai a zuba magi da kori da garin tafarnuwa da dafaffen gandar, bayan ya dan tafasa sai a zuba ganyen Ugwun a jira na tsawon minti uku zuwa hudu sannan a kwashe.