Masu ababen hawa a Abuja su na gogoriyon sayen man fetur da zai dauke su tsawon lokaci bayan wayi garin Talata da yawancin gidajen mai a rufe.
Aminiya ta ga dogayen layukan ababen hawa a wasu daga cikin gidajen man da aka bude Abuja, inda mazauna ke zullumin yiwuwar karancin mai sakamakon tashin hankalin da zanga-zangar #EndSARS ta haifar.
- #EndSARS: Ganduje ya nemi taimakon Rarara da Ali Nuhu
- Ta rasa ranta yayin wawason kayan tallafi a Kaduna
Wasu daga cikin masu ababen hawan sun ce tun da sanyin safiya suka je domin su sha mai saboda tun da dare suka lura da alamun karancin mai a gidajen.
Ana iya tunawa a makon jiya Kungiyar Dillalan Man Fetur ta IPMAN ta yi gargadin yiwuwar samun karancin man fetur a Najeriya.
IPMAN ta ce hakan zai iya faruwa ne sakamon harin da masu zanga-zangar #EndSARS suka kai wa motocin dakon mai da wuraren ajiyarsa.
Sai dai sanarwa da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC) ya fitar a safiyar Tatala ta ce babu kamfanin na da isasshen mai a rumbunsa kuma bukatar fargabar da masu ababen hawa ke yi.
“NNPC na tabbatar muku cewa yana da sama da Lita biliyan biyu na man fetur a ajiye domin tabbatar da ba a samu karancinsa ba daga yanzu har zuwa kwana 60 masu zuwa, saboda haka bukatar sayen mai saboda fargaba da ake yi”, inji sanarwar.