Duba da yadda ake samun karuwar bude makarantu masu zaman kansu a jihar Kwara, Majalisar Dokokin Jihar ta yi kira da a tsananta bin dokokin kafa makarantun a jihar.
Majalisar ta nuna damuwarta kan tumbatsar makarantun kudi da ake samu a jihar, wanda a cewarta hakan zai iya yin illa ga ingancin ilimi a jihar.
- Barazanar harin ta’addanci ta jawo rufe kasuwanni a Neja
- Zargin sakin tsohon Kwamishinan da ya ‘kashe’ abokinsa ya jawo zanga-zanga a Bauchi
Da yake mika korafinsa kan batun yayin zaman majalisar a ranar Talata, Honarabul Abdullahi Danbaba na jam’iyyar APC, ya ce, rashin aiki ya sa matasa da suka kammala karatu a jihar suka shiga bude makarantu ba tare da cika ka’idoji ba.
Ya ce akwai bukatar Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta dada matsa kaimi wajen tabbatar da ana cika sharuddan da aka gindaya kafin bude makarantun.
Korafin na Danbaba ya samu goyon bayan takwarorinsa a majalisar inda da yawansu suka ce dole gwamnati ta sa ido a kan batun don gudun gurbacewar ilimi a jihar.
Shugaban Majalisar, Honarabul Yakubu Salihu, ya bukaci Ma’aikatar Ilimin jihar ta tabbatar da ana kiyaye ka’idojin da aka shimfida kafin bude makarantun.
(NAN)