✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake bikin mika wa Sarkin Zazzau sandar mulki

Jama'a sun yi wa Zariya tsinke don shaida bikin ba Sarkin Zazzau Ahmad Bamalli sanda.

Abubuwa sun kankama inda manyan baki suka hallara domin shaida bikin ba wa Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu sandar mulki.

Dubun dubatar mutane da suka hada da sarakuna, kusoshin gwamnati, ‘yan siyasa, attajirai, mawaka, matasa maza da mata sun yi wa Birinin Zariya tsinke domin halartar gagarumin bikin.

Nadin Sarki Ahmadu Bamalli na zuwa ne shekara 100 rabon da a yi irinsa a gidan da ya fito daga cikin gidajen Sarautar Zazzau —Gidan Katsinawa.

Rabon Gidan Katsinawa da rike Sarautar Zazzau tun zamanin kakakn Sarki Ahmad Bamalli, wato Sarkin Zazzau na 13, Sarki Alu Dan Sidi wanda ya rasu a shekarar 1920.