✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ake adana kayan abinci masu saurin lalacewa har su dade

Hanyoyin da za a adana kayan abinci saurin lalacewa domin

Akwai kayan abinci da ke da surain lalacewa, kama daga kayan gwari, kayan marmari da kayan lambu.

Akan ce cefane ba ya yawa. Sai dai wani lokaci mutum kan yi cefane da nufin amfani da su, amma saboda wasu dalilai yana bukatar adana su kafin lokacin amfani da su, sai dai kuma yana tsoron za su iya lalacewa kafin lokacin.

Ga hanyoyin da za ku iya adana wadannan abinci cikin sauki, ba tare da sun lalace ba:

A adana a wuri mai sanyi

Dankali: Idan ba a iya adana dankalin Hausa ko na turawa ba yana rubewa saboda ruwan da ke cikinsa.

Yadda ake adana dankalin Hausa shi ne a ajiye shi a wurin da babu ruwa kuma da babu rana sosai.

A guji a ajiye shi a cikin firiza saboda yana iya daskarewa ko ma ya lalace.

Kada a ajiye albasa da dankali a waje daya saboda albasa kan jawo tsiro a jikin dankali.

Kabewa: Ajiyarta ba abu ne mai wahala ba, idan har ba a yanka kabewar ba. Amma idan an riga an yanka ta, sai ya yanka ta ’yan kananana a saka a firinji.

Kwai: Za a iya ajiye kwai a waje mai sarari inda iska za ta rika kadawa, inda babu zafi ko rana za ta taba shi.

Kwai baya son zafi, idan mutum na da firinji to ta kwana gidan sauki, amma ba a wurin kankara za a sa ba.

Ayaba/agada: Saboda saurin yaushi da ayaba da agada (plantain) ke yi, sai a ajiye su a wurin ba babu zafi ko rana, idan suka kai iya nunan da ake so, sai a sanay su a firinji.

Albasa: a ajiye albasa a inda babu ruwa, idan ya taba ruwa yanada saurin rubewa. Kada a hada shi da wani fruit saboda warin albasa yana da karfi kuma yana kama abubuwa mussamman ’ya’yan itatuwa.

Sanyawa a a firinji

’Ya’yan itatuwa: Wasu nunannun ’ya’yan itatuwan na da saurin lalacewa, saboda haka idan ana so su su dade, sai a saka su a waje mai sanyi ko a cikin firinji.

 

Dafaffiyar shinkkafa: Danyar shinkafa ba ta da matsalar ajiya, muddin ba a wuri mai ruwa aka sa ta ba, amma dafaffiyar shinkafa tana bukata a sanya ta a firinji ko a firiza.

Dafaffiyar shinkafa na iya kwana daya a firinji, amma idan a firiza ne za ta iya kaiwa kwana 10 ba tare da ta lalace ba.

Kar a ajiye dafaffiyar shinkafa a waje mai zafi domin yana iya sawa ta yi yauki.

Karas da gurji: Karasa na iya yin mako biyu zuwa uku a firinji. Gurji kuma zai na iya mako daya a firinji, saboda yana da saurin barci kuma baya jure zafi ko rana.

An fi so mutum ya sayi iya daidai wanda zai yi amfani da shi saboda kar ya rube ko kafin a yi amfani da shi.

Cucumber shi ne gurji da Hausa

Kayan ganye da na salak: Idan za a ajiye ganyen latas, kabeji, na’ana’a, ganyen kori, yakuwa, zogale, alayyaho da sauransu a sai a samu roba mai marfi, a kasan robar sai a sa takardar tishu a zuba da dan ruwa, sai a dora ganyen a kai.

Daga nan sai a sanya robar a cikin firinji, wannan ruwan da aka sa a ciki zai hana ganyen yin yaushi da sauri.

Za kuma a iya yanka ganyen shuwaka da alayyaho kanana yanda za a saka a miya, sai a kulla a leda a sa a firiza.

Daga lovefood.com

%d bloggers like this: