✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka yi wa hedikwatar APC tsinke yayin shigar Abdullahi Adamu Ofis

Sanata Adamu ya shiga ofis da safiyar Laraba

Sabon zababben shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya kama aiki a sakatariyar jam’iyyar ta kasa.

Sanata Adamu wanda tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa ne, ya isa gidan Buhari wanda a nan sakatariyar jam’iyyar take da misalin karfe 11:00 na safiyar Laraba.

Dandazon magoya baya sun yi wa sakatariyar tsinke don nuna murnarsu da goyon baya ga sabon Shugaban na APC.

Sanata Adamu ya zama sabon shugaban jam’iyyar ne ranar Asabar din da ta gabata, bayan kammala Babban Taron jam’iyyar na kasa, tare da samun goyon bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Wannan shi ne karonsa na farko da ya bayyana a hedkwatar jam’iyyar tun bayan zamansa sabon shugabanta.