An kammala Sallar Jana’izar Alafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi na Uku, babban basaraken Yarbawa da ya rasu yana da shekara 83.
Babban Limamin Kasar Oyo, Sheikh Moshood Ajokidero, shi ne ya jagoranci Sallar Jana’izar da misalin karfe 11.55 na safe a garin Oyo.
Manyan limamai shugabannin siyasa da sauran manyan mutane sun halarci jana’izar basaraken, wanda da la’asar, misalin karfe hudu na yamma za a kai shi makwancinsa a makabartar sarakuna da ke Baare.
Wasu majiyoyi sun ce za a kai shi makabartar ce bayan an kammala wasu al’adu.
Oba Lamidi Adeyemi, ya rasu ne bayan shafe shekara 52 a kan karaga, wanda ya mayar da shi mutum mafi dadewa a kan sarautar ta Alafin na Oyo.
Basaraken mai shekara 83, ya rasu ne da miasalin karfe 11 na dare, kafin wayewar garin Asabar, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Afe Babalola da ke Ado-Ekiti, Jihar Ekiti.
Marigayi shi ne Alafin na uku da ya jagoranci Masarutar Oyo daga zuriyar gidan Sarautar Alowolodu.
Oba Lamidi Adeyemi shi ne babban basarake na uku a Masarautar Oyo da ya rasu cikin wata biyar da suka gabata.
A ranar 12 ga Disamban 2021, Soun na Ogbomoso, Oba Jimoh Oyewumi, ya riga mu gidan gaskiya, sai kuma Olubadan Saliu Adetunji, ranar 2 ga Janairu, 2022.
Sakamakon rasuwar Alaafin, ragamar gudanar da harkokin dafar za ta koma hannun Shugaban Oyomesi, Basorun na Oyo, Babban Cif Yusuf Akinade Ayoola, har a nada sabon Alafin.