✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Egbetokun, ya ce rashin kyakkyawan shiri yayin raba tallafin ne ya jawo rikici, wanda ya kai ga asarar rayuka. 

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya bayar da umarnin a binciki lamarin turmutsitsin da ya faru a Oyo, Anambra, da Abuja.

Wannan na cikin wata sanarwa da Sufeto-Janar ɗin ya fitar a ranar Alhamis.

Egbetokun, ya ce rashin kyakkyawan shiri yayin raba tallafin ne ya jawo rikici, wanda ya kai ga asarar rayuka.

Ya gargaɗi masu shirya taruka cewa sakaci babban laifi ne, kuma dole ne a haɗa kai da jami’an tsaro don hana faruwar irin wannan abin tashin hankali.

Sama da mutum 35 waɗanda yawancinsu yara ne, suka rasu a wani turmutsutsi da ya faru a bikin masarauta a Ibadan.

Haka kuma, irin wannan iftila’i ya faru a Anambra da Abuja wajen rabon shinkafa, wanda ya jawo asarar rayukan mutum 30.

Sufeto-Janar ya yi kira ga masu raba tallafi da shugabannin al’umma su tabbatar da kyakkyawan tsari a nan gaba.

Hakazalika, ya yi gargaɗin jama’a su kula da lafiyarsu a irin waɗannan wurare.