Shugaban Majalisar Koli ta Shari’ar Musulunci a Najeriya, kuma tsohon mai neman takarar shugabancin kasa a karkashin inuwar jam’iyyar SDP, Dokta Ibrahim Datti Ahmed, ya rasu.
Dokta Ibrahim Datti Ahmed ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Alhamis a Kano bayan ya sha fama da rashin lafiya, kamar yadda iyalansa suka bayyana.
- Najeriya A Yau: Tattalin Arziki: Yadda 2021 Ta Zo Wa ’Yan Najeriya
- Yadda aka cafke kasurgumin dan bindigar Zamfara, Mai-’Yanmata, aka kubutar da mutane
Idan ba a manta ba shugaban majalisar kolin, na daya daga cikin wadanda tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya sa a cikin kwamitin da za su tattauna da Boko Haram kan tsagaita wuta a 2013, amma ya ki amsar tayin.
Dokta Ibrahim Datti Ahmed ya tsaya takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar SDP a lokacin Jamhuriyar ta uku.
An yi jana’izarsa a Masallacin Juma’a na Alfurqan da ke Kano, sannan aka binne shi a Makabartar Tarauni da ke birnin Kano.
Ya rasu ya bar ’ya’ya 10 da jikoki; daga cikin ’ya’yansa akwai Dokta Mukhtar Ibrahim Datti Ahmad, wani babban likita da ke zauna a Birtaniya.