’Yan Najeriya 808 ne suka fada tarkon masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa a sassa daban-daban na kasar cikin watanni bakwai da suka gabata – a tsakanin watan Janairu zuwa Yulin 2020.
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ya gano cewa baya ga kudin fansa na naira biliyan 4 da miliyan 200 da masu garkuwa suka nema cikin watanni bakwai, naira biliyan 96 aka batar domin biyan wannan bukata ta karbo fansar mutanen.
A halin yanzu ta’addancin garkuwa da mutane ne mafi girman barazana ga duk rukunoni na al’umma, kama daga baki zuwa mashahurai, attajirai da kuma talakawa.
Ruwan dare
Duk da cewa a shekarun baya wannan ta’ada ta fi shahara a yankin Neja Delta, inda tsageru ke yin garkuwa da mutane da manufar cimma wani buri na siyasa ko neman kudi, a yanzu babu inda ba ta karade ba a fadin kasar.
Ko da yake rundunar ‘yan sanda ta cafke daruruwan masu garkuwa da mutane a sassa daban-daban na kasar cikin tsawon watanni bakwai din da binciken ya gudana, har ya zuwa yau ba ta ba da bayanai ba game da hukuncin da aka zartar musu.
Masana doka da shari’a wadanda suka gana da wakilanmu sun lura cewa akwai dokoki da aka tanada don hukunta laifukan garkuwa da mutane, kuma ba su da rana matukar ba a aiwatar da su.
A cikin watanni bakwai din da aka gudanar da bincike a kansu, an gano cewa garkuwa da mutane ta auku a jihohi 33 na kasar, wadanda suka hada da Abia, da Adamawa, da Anambra, da Bauchi, da Bayelsa, da Binuwai, da Borno, da Kuros Riba, da Delta, da Ebonyi, da Edo, da Ekiti, da Enugu da kuma Yankin Babban Birnin Tarayya.
Inda matsalar ta fi kamari
Sauran su ne Imo, da Jigawa, da Kaduna, da Kano, da Katsina, da Kogi, da Kwara, da Legas, da Nasarawa, da Neja, da Ogun, da Ondo, da Osun, da Oyo, da Filato, da Ribas, da Sakkwato, da Taraba da kuma Zamfara.
Kididdigar da aka yi a kan jihohin ta nuna cewa ta’addancin garkuwa da mutane ya fi kamari a jihohin da ke yankin Kudancin Kudu, sai kuma yankin Arewa ta Tsakiya ya biyo baya a mataki na biyu.
Haka kuma yayin da ta’addancin ya tsananta, yankin Arewa Maso Yamma ya zo a mataki na uku, inda yankin Arewa Maso Gabas ya zo a mataki na biyar.