Karar harbe-harben bindiga ta firgita mazauna a yayin da kungiyoyin asiri ke yi musayar wuta tsakaninsu a yankin Ikorodu na Jihar Legas.
Mazauna sun ce ’yan kungiyoyin asiri na Eiye da Aiye Confrantaty masu gaba da juna sun yi sa’o’i sun harbe-harbe ranar Talata da dare a unguwar Owode-Elede da ke Ikorodu inda daukacin yankin da kewayensa ya shiga cikin zullumi.
- Lokuta hudu da Rahama Sadau ta jawo cece-kuce a Kannywood
- Dubun mai sayar da takardar daukar aiki ta bogi ta cika
- Kungiyar shirya fina-finai ta dakatar da Rahama Sadau
Shaidu sun ce kungiyoyin asiri masu gaba da juna sun yi mako biyu suna yakar juna tare da kashe mutane da yawa da kuma raunata wasu.
Wani mazaunin Owode, ya ce harbe-harben ya ritsa da shi ne a lokacin da yake hanyarsa ta komawa gida daga wurin aiki a daren Talata amma ya kasa saboda babu motsin motoci.
Ya ce, “Akwai babban tashin hankali a Owode Elede da ke kan titin Ikorodu inda wadanda ake zargin ’yan kungiyar aisiri ne ke yakar juna; Babu motsin ababen hawa da ke zuwa da dawowa daga Ikorodu.
“Motoci sun tsaya cik, musamman masu zuwa Ikorodu har zuwa Ketu, dsa Ojota, ga shi ’yan daba (Area boys) na taruwa a yankin Mile 12.
“Ana fargabar za su iya amfani da cunkoson ababen hawan da rikicin kungiyoyin asirin ya haddasa su yi wa mutane kwace.
“Na samu na bar wurin da kyar bayan na kira Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, Muyiwa Adejobi da takwaransa na Rundunar Ko-ta-kwana ta RRS; Yanzu zan koma Ketu zan kwana a wurin wani dan uwana tunda babu abun hawa”, inji shi.