✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka tilasta ne komawa bautar dodo bayan shiga addinin Kirista – Danmalikin Chawai

A karshen makon jiya ne ’ya’ya da jikoki da ’yan uwa da abokan arziki suka shirya wa Danmalikin Chawai kuma tsohon Hakimin Mai Zanko da…

A karshen makon jiya ne ’ya’ya da jikoki da ’yan uwa da abokan arziki suka shirya wa Danmalikin Chawai kuma tsohon Hakimin Mai Zanko da ke Masarautar Chawai a Karamar Hukumar Kauru da ke Jihar Kaduna Malam Kure Dawa bikin taya shi murnar cika shekara 120 a duniya. Bayan kammala bikin wakilinmu ya tattauna da shi, kan tarihin rayuwarsa da gwagwarmayar da ya sha.  Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

Mene ne tarihin rayuwarka a takaice?

To an haife ni ne a kauyen Pari Chawai da ke Karamar Hukumar Kauru a Jihar Kaduna a 1899, wato shekara 120 da suka gabata. Amma asalin mahaifina mutumin garin Damakasuwa ne, kuma gidan mahaifinmu gidan sarauta ne domin su ne asalin wadanda suka kafa garin. Sunan sarautar gidan shi ne Mai Zanko, zama ne ya kai mahaifinmu Pari Chawai. Ita kuma mahaifiyata asalinta ’yar kauyen Kiffin Chawai ne, duk a Karamar Hukumar Kauru.  A wannan kauye na Pari Chawai na girma, daga baya na dawo kauyen Kiffin Chawai na yi aure, bayan shekara daya da yin auren, sai matar da na aura ba ta sami ciki ba. Sai wani tsoho ya ce a bar ni in dawo garin Damakasuwa in yi kwana uku a bisa al’adar kabilar Chawai. Bayan da na dawo da matar na yi kwana uku, na koma nan take sai ta dauki ciki.

Na auri mata daban daban har guda 9, na haifi ’ya’ya 45, wadanda suke raye yanzu guda 25 ne. Kuma yanzu ina da jikoki 118 da tattaba kunne 199.

Kana da wayo lokacin da Turawa suka zo wannan yanki?

Kwarai ina da wayo Turawa suka zo wannan yanki na Chawai. Kuma Turawan sun zo ne da wa’azin addinin Kirista domin jama’armu su karba. A lokacin mutanenmu na yankin Chawai ba su karbe su ba. Sai daga baya suka karbi Turawan da addinin Kiristan da suka zo da shi.

Kuma ina daya daga cikin wadanda suka fara karbar addinin Kirista a yankin. A lokacin da na shiga addinin Kirista, sai da aka rika daure ni ana kewaya wuta da ni, saboda na fita daga addinin dodo na shiga na Kirista. A lokacin dole na fita daga addinin Kirista saboda azabtarwar da ake yi mini kullum. Na koma bautar dodo na zama Magajin Dodo na zama Madaukin Dodo. A lokacin ina zaune a Kiffin Chawai ne. Sai daga baya na sake komawa addinin Kirista. Na ci gaba da yi wa jama’a wa’azi. Farko na fara bin ECWA ne daga baya na koma Katolika, mu biyu muka kawo Darikar Katolika wannan yanki.

Mu ne muka fara gina wani dan daki a Kiffin Chawai muna  ibada, sai dakin ya yi kadan, daga nan na je na sayi itace a Kataf aka yanka katako, na sayi kwanon rufi muka gina babban coci muka rufe.

Daga baya na dawo gida Damakasuwa na ci gaba da aikin yada bushara, ni na fara bai wa babban fadan da aka kawo wannan gari mai suna Fada Jerry wurin da aka fara gina coci a garin.

Na tafi Bom a Jos saboda rashin lafiyar gyambon ciki da ke damuna, lokacin babu asibiti. Na je na yi shekara daya a can, bayan na samu sauki, sai na shiga taimaka wa mata masu haihuwa a fannin maganin gargajiya. Lokacin har Turawan na ba su mamaki suka ce in gaya musu maganin da nake diba nake bai wa mata masu haihuwa suna haihuwa lafiya, ba tare da wata matsala ba.

Lokacin idan mace ta kasa haihuwa ko ta haihu mahaifa ba ta fita ba, da na shafa magani a hannuna sai in fitar da mahaifar. Nakan sa hannu in cire yaro daga cikin mace ba tare da ta ji zafin komai ba. Kuma ina gwada wani abu ga mace mai ciki, idan yaran biyu ne ina ganewa. Da na dawo gida sai aka zo ana dauka ta a ko’ina a yankin, dare da rana ina taimaka wa mata masu ciki wajen haihuwa. Na taimaka wa daruruwan mata masu ciki.

A wane lokaci ne aka nada ka Dagacin Zanko?

Kamar yadda na fada maka tunda farko gidanmu a Damakasuwa gidan sarauta ne. Don haka an nada ni Dagacin Zanko a 1995, kuma a fadar Sarkin Zazzau da ke Zariya ne aka nada ni. Na rike wannan sarauta har zuwa shekara ta 2001. Kuma an nada ni Hakimin Gundumar Mai Zanko a shekarar 2001, zuwa shekarar 2017 da aka rushe mu.

Yaya za ka kwatanta yadda sarauta take a da da yanzu?

Ai yanzu babu sarauta, domin a da babu kudi a maganar sarauta. A da in mutum ya yi laifi za a yi masa hukunci, komai girmansa amma yanzu idan mutum yana da kudi komai rashin gaskiyarsa, babu abin da za a yi masa.

Yaya za ka kwatanta mutanen da da na yanzu?

Mutanen yanzu babu abin da suka rike sai mugunta. Mutanen yanzu ba su da gaskiya sai miyagun abubuwa, don haka komai ya lalace. Amma mutanen da ba haka suke ba, domin akwai gaskiya da rikon amana.

A da idan wani abu ya faru a tsakanin mutane akan yi hakuri da juna.Yanzu za ka ga dan uwanka ne zai yi maka mummunan abu. Yanzu za ka ga idan aka kawo maka hari, sai ka ga da hanun dan uwanka ko kuma ’ya’yanka. A da ana zaune lafiya amma yanzu babu zaman lafiya. Yanzu ana cewa an shiga wani lokaci na ilimi, alhalin ilimin na cuta ne. Ni ban ga amfani ilimin da mutanen yanzu suke da shi ba, domin ilimin yanzu, ilimin cuta ne. Mutanen da ba su da ilimi, amma akwai gaskiya da rikon amana. A da idan yaro ya yi ba daidai ba, za ka hukunta shi ko ba danka ne ba. Amma yanzu da ka dubi yaron wani, sai baban yaron ya ce me ya sa kake sanya ido ga dana?

Me za ka ce kan wannan biki na cika shekara 120 da ’ya’ya da jikokinka suka shirya maka?

A gaskiya na ji dadin wannan biki da aka shirya mini, saboda dadin da na ji ko a yau na mutum, na gode Allah.