✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda aka saki wanda ya kitsa sace dana’

Wani magidanci da aka sace dansa a Zariya domin neman kudin fasa mai suna Suleiman Haruna ya zargi ’yan sanda da sake wanda ya kitsa…

Wani magidanci da aka sace dansa a Zariya domin neman kudin fasa mai suna Suleiman Haruna ya zargi ’yan sanda da sake wanda ya kitsa sace dan nasa inda ya bukaci Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufa’i ya taimaka masa domin rayuwarsa da ta iyalansa tana cikin hadari sakamakon sako babban wanda ake zargin da kitsa sace dannsa. An sace dansa Muhammad Suleiman dan shekara biyar ne wanda daga baya aka same shi a yankin Toro da ke Jihar Bauchi.

Mahaifin yaron ya bayyana wa Aminiya cewa, “An kama wadanda ake zargi kuma ’yan sanda sun gudanar da bincike a kansu, amma ba tare da an kai su kotu ba sai ga shi an sako Nuhu Abubakar wanda aka fi sani da Yellow yana ci gaba da sana’arsa a PZ da ke Sabon Garin Zariya, kuma har barazanar kai kara kotu yake yi wai an bata masa suna.”

Mahaifin ya ce bayan sun ta fi Bauchi sun taho da wadanda ake zargin zuwa babban ofishin ’yan sanda na Jihar Kaduna, ba tare da bata lokaci ba suka tabbatar wa ’yan sanda masu bincike cewa su ne suka sace Muhammad Suleiman suka tafi da shi Toro da ke Jihar Bauchi.

Wadanda ake zargin su ne Nura da Sani kuma sun ce ta dalilin Yellow ne suka san Suleiman Haruna mahaifin yaron sanadiyar cinikin fili da suka yi da shi.

Sun kuma yi bayani cewa shi Yellow ne yake ba su bayanin kadarori da dukiyar Suleiman Haruna kamar yadda suka bukace shi da ya sayar da wasu domin ya fanshi dansa mai shekara biyar Muhammad Suleiman.

A cewarsa babban abin mamaki a kan wannan lamari shi ne yadda ’yan sanda masu bincike suka wanke Nuhu Yellow suka sallame shi kan wai ba ya da masaniyar sace yaron duk da bayanan da aka gabatar.

Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna DSP Yakubu Aliyu Sabo a kan korafin mahaifin yaron, sai ya yi alkawarin hada wakilinmu da wadanda ake zargi da sace yaron a Zariya don tattaunawa da su, tare da bayyana cewa adalci shi ne idan har da sa hannun wani da ake zargi, doka za ta yi hukunci daidai da abin da ya yi, in kuma bincike ya nuna babu sa hannunsa adalci shi ne a sake shi. Amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto bai kira ba.