Mutane 10 ne ake fargabar ’yan bindiga sun sace a unguwar Dutsen Alhaji da ke Abuja kafin wayewar garin Litinin din nan.
Gabanin Sallar Isha’ ranar Lahadi ’yan bindiga suka kutsa Rukunin Gidaje na Sagwari da ke unguwar suka sace mutane.
Mazauna unguwar sun ce akalla mutane takwas ne ’yan bindigar suka sace su a harin.
Wata majiyar ta ce mutanen da aka sace sun hada da mazauna unguwar mutum takwas, da kuma ma’aikatan wani otel su biyu.
- Badakala: Tinubu ya sa a binciki ministar Jin-kai, Betta Edu
- NAJERIYA A YAU: Dabarun Kauce Wa Talauci A Watan Janairu
Wani mazaunin rukunin gidajen, Muhammad Hassan, ya shaida wa Aminiya cewa, “Da misalin karfe 7.30 na dare, kafin Isha’ suka shigo rukunin gidajenmu dauke da muggan makamai.
“Daga tsaunin da ke bayan unguwar tamu suka bullo, inda suka shiga wasu gidaje suna yin awon gaba da mutane.
“A wani gida sun kwashi mutum biyar.”
Wani dan unguwar ya ce, “Yarinyar gidan da ta bude kofa a lokacin da maharan suke kwankwasawa, ta tsere zuwa wani otel da ke kusa da su.
“Sai suka bi ta ciki, ba su gan ta ba, amma sai suka tiso keyar mai tarbar baki da wani namiji da ke sayar da giya a otel din.”
Muhammad ya ce, “Sun yi kokarin shiga wasu gidajen, inda suka rika kwankwasa kofofin, amma da suka ga mutane na fitowa sai suka wuce da waɗanda ke hannunsu, suka koma ta tsaunin suka tafi da su.”
Wani dan unguwar, ya ce, “An yi wa ’yan sanda kiran gaggawa, amma kafin su zo ’yan bindigar sun tsere da mutanen da ke hannunsu.”
Kawo yanzu dai hukumar ’yan sanda ta birnin Tarayya ba ta ce komai kan harin ba.