✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka sace matafiyan Taraba 19 a Nasarawa

A daren Juma'a ne dai motar matafiyan ta fada tarkon ’yan bindigar da suka tare hanya a yankin Eggon da ke Jihar Nasarawa.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu matafiya 19, har da direbansu a hanyarsu ta zuwa Abuja daga Jihar Taraba.

Muatafiyan da suka hada da mata da kananan yara, dukkansu daga Jihar Taraba, na cikin wata bas din haya samfurin Hummer ne lokacin da suka fada a hannun masu garkuwa da mutane.

A daren Juma’a ne dai motar fasinjojin ta fada tarkon ’yan bindigar da suka tare hanya a yankin Eggon da ke Jihar Nasarawa.

Daga nan ’yan ta’addan suka yi awon gaba da daukacin mutanen zuwa cikin daji, har da direban motar, sannan suka kawar da motar daga wajen.

Mallakin motar ya tabbatar wa wakilinmu na Jalingo da faruwar lamarin.

Ya kara da cewa maharan sun fara tuntubar iyalan matafiyan suna neman kudin fansa.

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Nasarawa, Mai-yaki Muhammad Baba, ya ce suna da labarin abin da ya faru kuma sun tura jami’ansu domin ceto fasinjojin.

Ya ce, “Tun misalin karfe 6 na safe muka tura jami’anmu na yaki da garkuwa da masu mutane tare da ’yan banga a yankin Karamar Hukumar Eggon domin kubutar da matafiyan.”

 

Daga Sagir Kano Saleh Magaji Isa Hunkuyi, Jalingo Umar Muhammed, 

%d bloggers like this: