Wata daliba da ke ajin karshe a fannin aikin Nas-Nas a Jami’ar Maiduguri mai suna Fatima Habu Usman ta fada hannun wadansu miyagu wadanda suka sace ta a Keke NAPEP sannan suka yi mata wanka da ruwan batir (guba) kafin su yar da ita a gefen titi.
dalibar mai kimanin shekara 25, bayanai sun ce ta hau Keke NAPEP daga tashar mota ta tsakiyar birnin Maiduguri (Post Office) zuwa tashar Baga inda za ta tsallaka ta shiga gidansu a Federal Lowcost.
Alhaji Abu Usman Maidoki Balbaya, shi ne mahaifin Fatima, kuma ya shaida wa wakilinmu cewa, “Duk da cewa har yanzu yarinyar ba ta iya bude baki ta shaida mini abin da ya faru da ita ba, to amma a ranar Juma’ar da ta gabata ce na tashi daga Masallacin Juma’a, sai na samu kira daga ’yan sanda cewa in zo maza-maza ga ’yata tana cikin wani mummunan yanayi suna so in je in same su saboda akwai bukatar a je asbiti.” Ya kara da cewa, “Shi ke nan sai na sa takalmana na tafi ina zuwa sai muka tafi Asibitin kwararru da ke Post Office, daga nan bayan likitoci sun yi iya kokarinsu sai suka ce mu je Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, sai muka je can inda a yanzu haka take jinya.”
Ya ce kafin nan jami’an tsaro sun shaida masa cewa ta hau Keke NAPEP aka watsa mata guba aka yashe ta a waje in da suka ci karo da ita shi ne suka dauko ta zuwa ofishinsu. Ya ce a saninsa Fatima ta tafi Jami’ar Maiduguri ne inda take karatun digiri kan aikin Nas, kuma tana shekarar karshe.
Alhaji Usman Maidoki, ya ce amma zai iya kasancewa ta tashi daga makaranta da dadewa ta tafi wani wuri ko kuma ta dawo gida ta tafi wata unguwar.
Game da ko ya gamsu da bayanin da jami’an tsaro suka yi masa cewa ga halin da suka tsince ta, Alhaji Abu Usman, ya ce “Eh to ka gani wannan yarinya dai har yanzu ba ta samu kanta ba, kuma in ba ita ba zai yi wuya a san takamaiman abin da ya faru da ita, su dai jami’an tsaro sun fada mini cewa ta hau Keke NAPEP din haya sun watsa mata guba sun jefar da ita a waje, su kuma suka same ta suka yi bincike Allah Ya sa suka samu lambar wayata suka kira ni, to yanzu maganar tana wurin jami’an tsaro kafin ta samu kanta su ci gaba da bincike.”
Alhaji Abu Usman, ya ce ko kadan ba ya tunanin abokan karatunta ne suka yi mata haka, domin kuwa a kowane lokaci suna tare mazansu da matansu suna cikin mutunci da taimakekeniya, domin tunda wannan abin ya same ta duk cikarsu suna ta tururuwa zuwa gaishe ta a nan asibitin. “Idan kuma aka ce batagari ne zan ce eh za a iya samun haka, to amma kuma ba zai kai ga wannan matsayi ba, domin akasarin matasa batagarin, a yanzu ba su cika neman hallaka mutum ba, sai dai su karbi abin da za su karba su rabu da mutum. Saboda wannan bala’i na Boko Haram da ya same mu ya taba kowa ba mai son wani abu ya faru da shi ko wani nasa. Idan kuma aka ce barayi ne to nafi zaton su ne suka aikata wannan aika-aika, amma sai Allah bai ba su ikon cika burinsu ba, mai yiwuwa suna so su sace ta ce, sai Allah bai yi ba,” inji shi.
Alhaji Abu Usman ya bayyana ’yarsa Fatima Habu da yarinya mai ladabi da biyayya da natsuwa da hankali kuma ba a taba raba ta fada da wani ba ko a makaranta. “Sannan wani abin duniya ba ya tsole mata ido da fatan Allah Ya ba ta lafiya,” inji shi.