✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka sace amare biyu a hanyar Abuja

'Ya'ya hudu mata aka sace wa Sarkin Hausawan Anguwan Azara, biyu daga ciki amare


A watan Maris za a yi bikin auren biyu daga cikin ’ya’ya mata huɗu na wani shugaban al’umma da aka sace a yankin Jere da ke Jihar Kaduna.

’Ya’yan Sarkin Hausawan Anguwar Azara a yankin na Jere da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, Malam Ibrahim Tanko, da matansa biyu ne ’yan bindiga suka sace ranar Larabar da ta gabata.

Sai dai kuma ’yan bindigar sun sako uwargidan Sarkin Hausawan bayan sun gano cewa tana da hawan jini.

Da yake tattaunawa da wakilin Daily Trust ta waya ranar Azabar, Malam Ibrahim ya ce ’yan matan biyu na tsaka da shirye-shiryen aurensu aka yi awon gaba da su.

Wasu ’yan bindiga ne dai dauke da muggan makamai suka yi dirar mikiya a gidan shugaban al’ummar.

‘Da kyar na sha’

A cewar Sarkin Hausawan, ranar Alhamis ’yan bindigar suka kira shi ta wayar wani daga cikin iyalansa suka bukaci kalmar sirri ta bude wayoyinsa biyu da suka diba yayin harin.

“Alal hakika a lokacin da na samu na tsere ta daya daga cikin kofofin gidan, na manta ban debi wayoyina ba, don haka ’yan bindigar suka yi awon gaba da su.

“To sai ranar Alhamis suka kira suka bukaci mabudin wayoyin”, inji shi.

Ya kuma ce tun bayan ba su mabudin sirrin, ba a sake jin komai daga ’yan bindigar ba.

Ya ƙara da cewa, “Amma har yanzu ina sa ran za su kira domin in ji me za su ce.

“Ina kuma kira ga jami’an tsaro da su taimaka su kwato min matata da ’ya’yana hudu wadanda ke hannun ’yan bindiga har yanzu”.

Ko da yake babu tabbas a kan haka, alamu na nuna cewa Sarkin Hausawan ne babban hadafin maharan.

Ba wannan ba ne dai karo na farko da ’yan bindiga suka kai hari a kan wani shugaban al’umma ko iyalinsa a Jihar ta Kaduna.