An rufe hannu daya na babbar hanyar Kaduna zuwa Zariya bayan wani yanki na titin da ke kusa da wata gada ya rufta.
A safiyar Litinin jami’an hukumar kiyaye hadurra (FRSC) a Jihar suka isa wurin da abin ya faru, inda suka tare hannun suna kuma mayar da masu ababen hawa zuwa daya hannun titin.
An samu ramin ne a titin da ke kusa filin Kasuwar Duniya na Kaduna mai makwabtaka da Unguwar Kaji.
Wani mazaunin yankin, Suleiman Umar, ya shaida wa Aminiya cewa wurin ya tsage ne bayan wasu tireloli dauke da siminti sun wuce, kafin daga baya ya burme gaba daya.
Umar wanda ya ce gabanin haka wurin ba shi da matsala ya ce ramin ya haifar da cunkoson ababen hawa har zuwa tsakar dare a kan titin. Hakan ta tilasata wa motoci komawa amfani da hannu guda yayin da masu babura ke lallabawa ta daya hannun da aka samu ramin.
Wata majiya kuma ta ce cunkoson ababen hawa da kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a yammacin ranar Lahadin ne suka haifar da ramin.
Tun da safiyar Litinin jami’an hukumar kiyaye hadurra (FRSC) a Jihar suka isa wurin da abin ya faru, inda suka tare hannun suna kuma mayar da masu ababen hawa zuwa daya hannun titin.