An gano cewa sai da gwamnati ta saki wani dan bindiga da ke hannunta kafin ’yan bindiga su sako daliban Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka da suka yi garkuwa da su.
Binciken na Aminiya ya gano cewa kafin su sakin daliban, sai da aka biya ’yan bindigar kudin fansa Naira miliyan 15 da suka bukata, amma suka yi ta wasa da hankalin masu shiga tsakani na kusan wata daya.
- Buhari na biyan ’yan bindiga kudin fansa —Obasanjo
- Juyin mulki: ‘Fadar Shugaban Kasa na cikin rudani’
- An kama dan bindiga ya kai hari a masallaci
Majiyoyinmu sun tabbatar mana cewa bayan karbar kudin fansar, sai wanda ya jagoranci garkuwa da daliban, mai suna Buderu, ya bijire, aka rika kai ruwa rana da shi.
Sai da aka hada da mahaifin wani gawurtaccen dan bindiga mai suna, mai lakabin Janar, ya shigo da dan nasa don ganin Buderu ya amince ya saki daliban.
Daga baya Buderu ya amince zai saki daliban ba tare da an kara musu kudi, amma bisa sharadin sai an sako wani dan uwansa mai suna Laulu da ’yan sanda suka kama da Dajin Falgore a Jihar Kano.
Majiyoyinmu sun shaida mana cewa a ranar Talata ne aka dauko Laulu daga wani ofishin ’yan sanda da ke Kano zuwa Kaduna, inda aka yi musayarsa da daliban.
’Yan bindigar sun mika wa masu shiga tsakanin ragowar daliban 27 ne a Kidandan, Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna, kwana 57 da yin garkuwa da su a ranar 11 ga watan Maris, 2021.
Gumi da Obasanjo sun taimaka
Fitaccen malamin Islama, Sheik Ahmad Abubakar Gumi ne ya shiga gaba wajen tattauna don ganin an sako daliban, da taimakon tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo.
Kafin nan, Sheik Guma da Obasanjo sun yi ganawa akalla sau biyu game da matsalar garkuwa da mutante da ke addabar Arewacin Najeriya wanda ke kara kamari a baya-bayan nan.
Sheik Gumi ya jagoranci wata ziyara zuwa ga Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, kafin daga baya Obasanjo ya shiyra musu liyafar bude-baki a gidansa da ke Abuja.
An gano cewa masu shiga tsakanin sun tuntubi Gwamnatin Tarayya ne domin a saki Laulu, wanda aka ce “tubabben mai satar shanu ne amma ’yan banga suka yi masa shig-shigo-ba-zurfi suka kama shi”.
Sabanin rahotannin farko da ke ta cewa dalibai 39 ne sace daga kwalejin, bayan sako ragowar 27 din, an bayyana cewa su 38 ne, amma daga cikinsu mutum daya ya tsere daga hannun ’yan bindigar washegarin ranar da aka sace su.
Ana iya tunawa cewa da farko masu garkuwar sun sako 10 daga cikin daliban a ranakun 5 da 8 ga watan Afrilu, bayan an biyu kudin fansa Naira miliyan 17.
Wadanda suka shiga tsakani
Majiyoyin tsaro sun shaida wa Aminiya cewa wadanda suka sanya baki wajen tattaunawar ’yan uwa da surukan ’yan bindiga ne, amma ba su hannu a aikata laifuka.
“Tun jiya (Talata) da dare muke nan tare da jami’an lafiya muna jiran isowarsu amma ba su zo ba, sai da safe masu shiga tsakanin suka kira cewa mu kasance cikin shirin karbar daliban 27,” inji majiyar.
Isowar Daliban Afaka Kaduna
Da zuwan daliban, aka wuce da su Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, inda Kwamishinan ’Yan Sanda, Umar Muri ya karbe su.
Aminiya ta lura cewa yawancin cikin daliban suna dingishi kuma babu alamar rashin koshin lafiya a tare da su.
Shugaban Kungiyar Daliban Kwalejin, Abdullahi Usman ya yi godiya ga duk wadanda suka taimaka aka ceto daliban.
Wani daga cikin iyayen daliban da ke kusanci da tattaunawar ya ce: “Sun kwana ne a gidan wani shugaban Fulani a wajen garin Kaduna.
“Da farko mun tura motocin da za su dauko su, amma wani abu ya faru, shi ya sa dole suka kwana a wurin.
“Muna godiya ga Sheik Ahmad Gumi, tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, jami’an tsaro da sauran wadanda suka ba da gudunmawa. Allah Ya kawar da sake faruwar irin wannan tashi hankali.”
Daga: Sagi Kano Sale, Lami Sadiq, Mohammed I. Yaba (Kaduna) da Peter Moses (Abeokuta)