Wata musayar wuta da aka yi tsakanin jami’an tsaro da wasu ‘yan bindiga a ranar Laraba da daddare ta yi sanadiyyar kashe wani jami’in hukumar tsaro ta DSS a kauyen Kalong na karamar hukumar Shendam a jihar Filato.
Jami’in, wanda aka bayyana sunansa a matsayin Barista Mukhtar Moddibo ya fito ne daga karamar hukumar Misau ta jihar Bauchi.
Yanzu haka dai gawar mamacin na can ajiye a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH).
Rahotanni sun nuna lamarin ya faru ne lokacin da hadakar rundunar tsaro ta sojoji da ke yankin ta ci karo da wani harsashi yayin ba-ta-kashin da ta yi da ‘yan bindigar.
Jami’an tsaron da su ka hada da na DSS a cewar rahotanni sun yi wa kauyen kawanya ne tun da farko suna neman jagoran ‘yan bindigar da ma tawagarsu, bayan sun sami bayanan sirri kan maboyar wasu masu hada-hadar bindigogi a yankin.
Daga nan ne kuma jami’an na DSS su ka kama wasu daga cikinsu da bindigogi kirar AK47 kafin faruwar iftila’in.
Lamarin kuma ya zo ne a daidai lokacin da jami’an tsaro su ka kara matsa lamba wajen kakkabe masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga da kuma sauran masu dauke da makamai da su ka addabi sassa da dama na jihar.
Ayyukan jami’an tsaron dai ya yi sanadiyyar kame wanda ya kashe wani malamin Jami’ar Jos, Dokta Joana Drenkat wanda wata kungiyar masu garkuwa da mutane su ka hallaka a kwanakin baya.