✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka kashe dan Majalisar Dokokin Kaduna a hanyar Zariya

Dan majalisar na daga cikin wadanda aka kashe a harin hanyar Kaduna zuwa Zariya.

Dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Ridwanu Aminu Gadagau mai wakiltar Mazabar Giwa a jihar, na daga cikin mutanen da ’yan bindiga suka kashe a hanyar Kaduna zuwa Zariya a daren ranar Litinin.
Aminiya ta gano yadda aka gano gawar dan majalisar daga cikin gawarwakin mutanen da ’yan bindigar suka kashe a ranar Laraba.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Yusuf Ibrahim Zailani ya tabbatar da rasuwar dan majalisar ta wata sanarwa da hadiminsa kan kafafen watsa labarai, Ibrahim Dahiru Danfulani, ya fitar.

Ya ce, “Muna cikin kaduwa da tashin hankali. A wannan lokaci muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan Gadagau, matashin dan majalisa mai burin kawo sauyi a majalisa a yankinsa da ma Najeriya. Za mu yi rashin ci gaban da ya ke kawo mana.”

Kakakin majalisar ya jajantawa iyalan dan majalisar tare da iyalan sauran sauran wadanda harin ya rutsa da su.

Kafin rasuwarsa, Gadagau shi ne Shugaban Kwamitin Kananan Hukumomi a majalisar dokokin jihar.

%d bloggers like this: