A yammacin ranar Talatar da ta gabata ce wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka harbe tsohon Babban Hafsan Tsaron na Kasa, Eya Cif Mashal Aled Badeh a yayin da yake dawowa daga gonarsa a hanyar Keffi zuwa Bade a Jihar Nasarawa.
Sanarwar da Kakakin Rundunar Sojin Sama, Ibukunle Daramola ya fitar ranar Talatar da daddare ta ce ’yan bindigar sun kashe Badeh ne a cikin motarsa lokacin da yake komawa gida daga gonar.
A cewar sojin, Mashal Badeh ya rasu ne sakamakon raunukan da ya samu daga harbin bindiga. An kashe Aled Badeh ne a cikin motarsa kirar Toyota Tundra mai lamba MUB 396 AA lokacin da wadansu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka harbe shi a kusa da garin Gitata da ke kan hanyar Keffi zuwa Bade da ke Jihar Nasarawa.
Wadansu mutanen garin Gitata da Aminiya ta zanta da su sun ce an kashe marigayin ne a kan hanyarsa ta dawowa daga gonarsa da ke tsakanin garin Koso da Kugwaru. Sun ce garin Mararabar Gurku ya fi kusa da gonar, amma saboda rashin kyan hanyar ya sanya dole a rika bi ta hanyar Panda da ke babbar hanyar Keffi zuwa Bade.
Ganau din sun shaida wa Aminiya cewa ba su san wane ne a cikin motar ba lokacin da aka harbe shi, sai da Rundunar Sojin Sama ta fitar da sanarwar cewa Iya Mashal Aled Badeh ne.
Wani dirabe mai suna Idris Musa ya wanda yake cikin wadanda suka fara kaiwa ga gawar ya bayyana wa Aminiya cewa lamarin ya auku ne da misalin karfe 6: 45 na yamma a ranar Talata lokacin da yake tuki zuwa Gitata daga Keffi, “Abin da na sani shi ne lokacin da muka zo kusa da Unguwar Mangoro sai aka tare mu aka ce mana barayi sun tsare hanya. Sai ga wannan motar kirar Tundra (wadda aka harbe Aled Badeh a ciki) ta wuce, da kunna wutar motar sai su kuma suka shiga harbe-harbe. Na ji karar harbi sama da goma, wanda hakan ya sa na ruga cikin daji. Daga baya sai aka fada mana za mu iya wucewa bayan abin ya tsagaita,” inji shi.
“Daga baya sai muka matsa, sai muka ga an riga an harbi wancan din (Aled Badeh) yana kwance a cikin mota, shi kuma direban an harbe shi a hannu, lokacin sojoji suna daga shi, suna kokarin daure masa hannu da bandeji,” inji shi.
Musa ya ce, “Na dade ina ganin irin wannan abu a wannan hanyar. Na saba ganin ana harbe-harbe. Har na taba ganin an harbi wani a kafa. Wannan ne karo na uku a cikin wannan wata da irin wannan tare hanya ana fashi ke faruwa, an kashe mutum biyu kuma aka sace daya a wannan wata.”
Da aka tambaye shi yadda ya gane wanda ake kashe cewa shi ne Aled Badeh, sai ya ce, bai san cewa gawar mutumin da ya gani ta tsohon babban soja ba ne.
“Ni dai na ga mutum babba a kwance ban san ko wane ne ba, sai daga baya na ji matsayinsa. Shi kuma direban an harbe shi, amma bai mutu ba. Ni dai na gan shi kato ne a kwance a cikin mota. Sai na dawo nan ne sai na ji ana fadar matsaynsa,” inji shi.
Game da batun cewa akwai shingen sojoji a kusa da inda abin ya faru, direban ya ce, “Gaskiya akwai shingayen tsaro na sojoji a kusa, amma suna dadewa ba su zo ba. Ko na ranar Talata ma sun kai kusan minti 15 ba su zo ba. Sai bayan ’yan bindigar sun shiga daji ne suka zo. Akwai shingen sojoji a Gitata da na Tudun Uku. Sojojin shingen Tudun Uku ne suka zo. Da muka zo wajen motar, mun samu sojojin suna taimakon direban.”
Wani mai suna Abdul Gitata ya bayyana wa Aminiya cewa sau uku ana kai masa hari a yankin, “Har sun taba harbina, kuma yawancin suna amfani ne da kakin soja. Idan suka fara harbi da ka tsaya sai su yi garkuwa da kai. Kuma sukan aikata wannan mummunar aika-aikar har da rana,” inji shi.
Da Aminiya ta tuntubi Sarkin Gitata, Turaki Danlami Rabo ya ce bai da damar yin magana a kan irin wannan lamari.
A yayin da dangi da iyalan mamacin suke ci gaba da zaman makoki, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kisan Mashal Badeh da babban abin bakin ciki, inda ya umarci hukumomin tsaro su zakulo makasan.
Shugaban a wata sanarwa da Kakakinsa Femi Adesina ya fitar ya yi ta’aziyya ga iyalan mamacin da abokan aikinsa sojoji da gwamnati da al’ummar Jihar Adamawa inda ya roki Allah Ya bai wa iyalnsa hakurin jure wannan babban rashi.
Babban Hafsan Sojin Sama Iya Mashal Abubakar Sadik ya ce Rundunar Sojin Sama tana aiki da sauran hukumomin tsaro domin zakulo wadanda suka kashe Mashal Aled Badeh don gurfanar da su a gaban shari’a.
Mashal Abubakar wanda ya yi magana a shekaranjiya Laraba a taron rubu’in shekara na hudu na Babban Hafsan Sojin Sama a Abuja, ya ce ba za su lamunci makasa su kashe tsohon Babban Hafsan Tsaro a kan hanya ba.
Ya ce, “Daukacin sojojin sama sun kadu, kuma suna mika ta’aziyya ga iyalansa kuma muna samun karin gwiwa kan tausayawar da ’yan Najeriya da dama ke nuna mana.”
Tuni dangi da iyalan marigayin da ke kauyen Bintim da ke Karamar Hukumar Mubi ta Arewa ya shiga cikin rudu sakamakon samun labarin kashe Mashal Badeh, inda ’yan uwa da dangi suka taru a gidan marigayin don zaman makokinsa cike da bakin ciki da jimami.