Fadar Shugaban Kasa ta ce ta kara sabon kasafin kudin Najeriya na 2020 ne da biliyan N216 domin aiwatar da muhimman ayyuka a yanayin cutar coronavirus.
Babban Hadimin Shugaban Kasa kan harkokin Majalisar Wakilai, Hon. Umar El-Yabub ya ce hakan zai rage tasirin annobar a kan ’yan Najeriya ya kuma bayar da damar yin muhimman ayyukan raya kasa.
“Mun bayar da muhimmanci ga ayyukan raya kasa da ke bukatar aiwatarwa da sauri da kuma yakar annobar COVID-19 da magance matsalolin da ta jefa ‘yan Najeriya a ciki, shi ya sa aka yi wa kasafin gyaran fuska”, a cewarsa.
Da yake yi wa ’yan jarida bayani bayan Buhari ya sanya hannu a kan kasafin, Umar El-Yakub ya ce gwamnati ta samu kudaden da take sa rai tare da hasashen samun karin wasu domin aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin.
Sabon kasafin kudin 2020
A ranar Juma’a 10 ga watan Yuli ne Shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan sabon kasafin na Naira tiriliyan 10.81 bayan Majalisar Tarayya ta amince da shi a watan Yuni.
A jawabinsa a lokacin sanya hannun, Buhari ya ce kudaden da za a kashe a sabon kasafin sun karu da Naira biliyan 216 daga Naira tiriliyan 10.59 da aka ware a baya.
Farashin gangar mai
Da farko Majalisar Tarayya ta amince da kasafin ne a kan farashin gangar danyen mai Dala 57 a watan Disamban 2019.
Daga baya gwamnatin ta yi masa kwaskwarima saboda faduwar farashin mai bayan bullar annobar COVID-19.
A bayaninsa, El-Yakub ya ce an kara kasafin ne domin rage tasirin annobar COVID-19 a kan ’yan Najeriya da kuma aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa.
“An fara kasafin 2020 ne a kan farashin mai Dala 25, amma yanzu an mayar da shi kan Dala 28 shi ya sa aka dan samu kari a kudaden shiga.
“Farashin da aka fara sawa Dala 53 ne, amma yanzu farashin ya dan karu, ko da yake adadin man da ake hakowa ganga miliyan 1.8 zuwz 1.9 a kullum.
Yadda za a yi da kasafin
“Game da karin da aka samu a kasafin ta fuskar farashin mai, tabbas an samu wasu kudaden, ana kuma hasashen samun wasu.
“Bayan nan, akwai bukatar a fahimci cewa an yi gyaran fuskar ne domin bayar da muhimmanci ga wasu ayyukan gwamnati ta yadda za a magance matsalar rashin ababen more rayuwa da kuma farfado da tattalin arziki da magance matsalolin da annobar ta haifar.
“An zuba kudade a wadannan bangarorin sannan akwai tallafin da Gwamnatin Tarayya ke so ta bayar a nan gaba.
“Wadannan su ne suka sa aka yi wa kasafin gyaran fuska domin a samu yin anfani da wasu kudaden da a baya aka ware domin wasu ayyukan da a wannan yanayi ba sai an gaggauta yin su ba.
Alakar majalisa da bangaren zartarwa
A cewarsa kyakkyawar alakar da ke tsakanin bangaren zartarwa da majalisa ta samu ne saboda shirin bangarorin biyu na hidimta wa ‘yan Najeriya.
Ya ce bangarorin biyu na da kyakkyawar fahimta da mutunta juna a tsakanninsu wajen kawo cigaban kasa.
Ya musanta zargin cewa Majalisar ’yar amshin shatar gwamnati ce, yana mai cewa bangarorin biyu suna yin aiki tare shi ya sa ba a samu tangarda ba a aikin kasafin kudin.
“Ba a saba ganin haka a majalisun baya ba. Shi ya sa ’yan Najeriya ke tunanin cewa majalisar na saurin amincewa da kudurori ko tantance wadanda za a ba mukamai. Gaskiyar magana ita ce a tare da su ake yin komai”, inji shi.