✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kama ni- Dino Melaye

  A safiyar yau ne jami’an Hukumar Shige da Fice suka kama sanata Dino Melaye a filin jirgin Nnamdi Azikwe da ke Abuja.   Bayan…

 

A safiyar yau ne jami’an Hukumar Shige da Fice suka kama sanata Dino Melaye a filin jirgin Nnamdi Azikwe da ke Abuja.

 

Bayan sun sake shi, sanatan ya yi bayanin abin da ya faru, inda ya ce “Da ni da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa sanata Ike Ekweremadu da wasu sanatoci mun shigo filin jirgi a kan hanyarmu ta zuwa kasar Moroko domin wani aiki.

 

“bayan na shigo an kammala bincike na. Bayan na je na zauna a wajen da matafiya suke zama suna jiran jirgi, sai kawai jami’an Hukumar Shiga da Fita suka kira ni wai ‘yan sanda sun kira su cewa ba zan iya yin tafiya ba.  

 

“sai na ce musu ba gaskiya bane domin ‘yan sanda Hadaka na duniya sun ce bas a nema na. Sai bude musu shafin rundunar ‘yan sandan Hadaka na duniya wato INTERPOL a yanar gizo na nuna inda suka karyata neman. Amma suka ci gaba da nanata cewa fa lallai ‘yan sanda suka ba su izini.

“sai suka ce in shiga ofishinsu. Daga nan sai suka fizge min katin tafiya, amma nan take na fizge abu na. sai suka zagaye ni wai suna jiran ‘yan sanda su fada musu me za su yi.”