An gurfanar da wani matashi mai kimanin shekara 25 a kotun shari’ar Musulunci da ke Fagge a Kano bisa zarginsa da mallakar wasu kulli 39 da ake zargin na Tabar Wiwi ne.
Matashin, mai suna Ibrahim Shehu, wanda mazaunin unguwar Kwana Hudu ne a birnin Kano, na fuskantar tuhumar mallakar Tabar ta Wiwi.
- An haifi yara 2.7m a Katsina cikin shekara 5 – Hukumar Kidaya
- ’Yan ta’adda sun dasa bom a makarantu da asibitocin Kaduna
Ko da yake wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa, amma alkalin kotun, Mai Shari’a Bello Khalid, ya ba da umarnin a garkame shi a gidan gyaran hali.
Tun da farko dai, dan sanda mai shigar da kara, Abdul Wada, ya shaida wa kotun cewa an cafke Ibrahim ne ranar 22 ga watan Fabrairun 2022 yayin wani sintiri.
Ya ce an kama shi ne wajen misalin karfe 8:00 na dare da kulli 39 na tabar, laifin da ya ce ya saba da sashe na 137 na Kundin Dokar Shari’ar Musulunci na Jihar Kano.
Daga nan alkalin ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 14 ga watan Maris domin yanke hukunci.