Dubun wani lauyan bogi ta cika a lokacin da yake tsaka da kare wanda ake zargi da aikata laifi a gaban kotu.
Asirinsa ya tonu ne a Kotun Majistare ta 6 da ke Ifo, Jihar Ogun, inda ya gabatar da kansa daga wani kamfanin shari’a, a gaban Mai Shari’a I. A Arogundade, a shari’ar da ke tsakanin Ifeanyi Chuckwu da Ayo Itori.
- Kotu ta aike da matashi gidan kaso bisa zargin fyade
- An kama wanda ya yi wa yarinya fyade har ta mutu
- Kotu ta daure lauyan bogi shekara uku
Yadda ya gabatar da kansa ya sa wa wani ma’aikacin kotun shakku inda ya tambaye shi matakin iliminsa da kuma shekarar da ya kammala Makarantar Kwarewar Lauyoyi.
Lauyan bogin ya ce ya kammala makarantar ne a shekara 2009, amma da aka bi jerin sunayen ’yan yayen shekarar babu sunansa.
Kakakin ’Yan Sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce bayan samun labarin ne Baturen ’Yan Sandan yankin Ifo ya sa aka kamo mutumin wanda ake kan bincika kafin a mika shi inda ya dace.
Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, a cewar Oyeyemi, ya nuna damuwa kan yadda ake yawan samun lauyoyin bogi masu damfarar mutane a jihar.
Oyeyemi, ya ce a watanni ukun da ya yi a matsayin Kwamishina ’Yan Sandan jihar an kama lauyoyin bogi fiye da biyar.
Ya yi kira ga Kungiyar Lauyoyi reshen ta jihar da ta dauki kwakkwaran mataki na ganin an hana faruwar hakan.