✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka hallaka ’yan Boko Haram da sabbin sansanoninsu a Borno

’Yan banga na lalata sabbin sansanonin Boko Haram da sojoji suka hallaka a yankin Mafa na Jihar Borno.

Dakarun sojin Najeriya daga Rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) tare da hadin gwiwar Civilian CJTF, sun kashe ’yan ta’addar Boko Haram a yankin Mafa na jihar Borno.

Wata majiyar tsaro ta ce dakarun sun yi artabu da mayakan kungiyar ne a wani samame, inda suka kashe ’yan ta’addan tare da tarwatsa sabbin sansanonin kungiyar guda shida, suka kwace manyan bindigogi da sauran makamai.

Majiyar ta ce sojojin sun hallaka hudu daga cikin ’yan ta’addan, sauran kuma suka tsere da kyar, dauke da raunukan harbi.

Ta ce dakarun sun kai farmakin ne bayan samun bayanan sirri kan maboyar ’yan ta’addan a yankunan Karkut da Koshobe.

Aminiya ta samu labarin cewa sojojin sun yi arangama mayakan ne a Karkut da kuma kauyukan kezemari da Ladinbuta.

Majiyarmu ta ce, ’yan banga na ci gaba da lalata sauran sansanonin ’yan ta’addan a yankin.

%d bloggers like this: