✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka gudanar da jana’izar Balarabe Musa

Babban yaron tsohon gwamnan ya ce za a yi jana'izar mahaifin nasu a masallacin Sultan Bello dake Kaduna.

An gudanar da sallar jana’izar ne bayan idar da sallar La’asar a masallacin Sultan Bello dake Kaduna, wanda Sheikh Ahmed Gumi ya jagoranta.

Masallacin ya samu halartar dandazon mutane daga ciki da kewayen Kaduna, inda mutane ke ta nuna alhininsu ga rashin tsohon gwamnan Kadunan.

Daga cikin wanda suka samu halartar jana’izar akwai tsofaffin gwamnonin Kaduna; Ahmed Mohammed Makarfi and Mukhtar Ramalan Yero, sai dai gwamnan jihar Mallam Nasir El-Rufa’i ya samu wakilcin (SSG) Balarabe Abbas Lawal.

Sanata Shehu Sani, shugaban alkalan Kaduan Mohammed Lawal, dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a 2019 Alhaji Lema Jibril, da Hon. Isah Mohammed Ashiru duk sun samu halartar sallar jana’izar.

Bayan idar sallar an dauke gawar mamacin zuwa makabartar Unguwar Sarki, wanda a nan ne aka birne shi.