✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Aka Fara Gasar Alkur’ani ta Kasa Karo Na 38 A Yobe

An fara musabakar Alkur'ani na kasa karo na 38 a Jihar Yobe

Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bukaci Musulmi su ci gaba da dabbaka gasar Gasar Karatun Al-Kur’ani saboda yadda gasar ke karfafa haddar Alkur’ani a duniya baki daya.

Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi wannan kira ne a taron kaddamar da Musabakar Karatun Al-Kur’ani ta Kasa Karo na 38 a Damaturu, Jihar Yobe.

Ya bayyana cewa gudanar da masabakar na habaka ilimin addinin Musulunci musamman a tsakanin matasa inda suke dagewa su karatunsa har su zama zakaru a duniyar Musulmi.

Sarkin Musulmi, wanda Shehun Borno Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin Ibn El-kanemi ya wakilta ya aba wa gwamnatin Yobe bisa daukar nauyi da kuma yadda aka raba bangaren maza da na mata wajen gudanar da gasar.

A jawabinsa na maraba a taron da ya gudana a Filin Wasa na 27 Augusta, shugaban kwamitin musabakar, tsohon gwamnan Yobe, Sanata Ibrahim Gaidam, ya yaba wa Jami’ar  Usmanu Dan Fodiyo da ke Sakkwato game da kokarinta wajen shirya gasar a matakin kasa.

Ya kuma jinjina wa kwamitocin gasar ta Alkur’ani dangane da yadda suka jajirce wajen ganin an gudanar da shi, kamar yadda aka bukata.

Daga nan ya Yi fatan kammala wannan gasa lafiya tare da neman cigaba da addu’ar neman zaman lafiya a duniyar musulmi da ma kasar mu ta Najeriya baki daya.

Mataimakin shugaban jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sakkwato, Farfesa Lawan Bilbis ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni bisa daukar nauyin gasar, da kuma yadda aka raba bangaren maza da na mata a wajen kaddamar da gasar.

Farfesa Lawan Bilbis ya mahaddatan da za su fafata a gasar da su kwantar da hankalinsu don ganin sun bi ka’idojin karatu kamar yadda Allah Ya shimfida, domin ta haka ne za su kai ga nasara.

A jawabinsa na bude gasar, Gwamna Mai Mala ya jaddada muhimmancinta ga al’ummar Musulmi saboda tana karfafa musu gwiwa wajen meman ilimin addini da kuma sanin ka’idojin karatun Alkur’ani.

Mai Mala ya bukaci iyaye da su hada hannu da gwamnati wajen fadakar da ‘yayansu game da muhimmancin zaman lafiya tsakanin da ninsatar harkokin ta’addanci.

Ya ci gaba da cewar, a kwanakin baya majalisar dokokin jihar ta yi dokar kafa Hukumar Hisba wadda nan take aka amince da ita, kasancewar samar da hukumar ta Hisba zai taimaka wajen gyara tarbiyya musamman a tsakanin matasa.