✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin mata da miji da yi wa matashi kisan gilla a Kano

Matar ta kashe matashin saboda ya yi yunkurin hana ta kashe kanta.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama wata matar aure bisa zargin ta da kisan wani matashi da suke zaune a gida daya a unguwa uku da ke yankin Karamar Hukumar Tarauni a jihar.

A cikin wata sanarwa da kakakin ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya sanya wa hannu, ya bayyana cewa matashin, wanda dan asalin Jihar Bauchi ne, ya rasa ransa ne sakamakon caka masa wuka da matar ta yi wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsa.

A cewar Kiyawa, lokacin da jami’ansu suka isa gidan, sun gano wukar da wacce ake zargin da ita ta yi amfani wajen kisan marigayin.

Sai dai a jawabinta na ikirarin aikata laifin, matar wacce ‘yar kimanin shekara 24 da haihuwa, ta bayyana cewa ta caka wa marigayin wuka ne daidai lokacin da yake kokarin hana ta kashe kanta da ta yi niyyar yi.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Muhammad Usaini Gumel, ta bayyana cewa a yanzu haka rundunar ta kama mijin matar da kuma maigadin gidan nasu, sakamakon taimaka wa wacce ake zargin don rufa mata asiri.

Rundunar ta kara da cewa a da zarar ta kammala bincike za ta gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya don girbar abin da suka shuka.

Tun da farko dan uwan marigayin Salisu Hafiz Gorondo ya sanar da ‘yan sanda game da abin da ya faru.

Ya bayyana cewa bayyan an fada musu rasuwar dan uwan nasu sai ya zo Kano, inda ya tarar a kafin su zo har an yi masa wanka.

Sai dai da suka zo sai suka ga jini na zuba a jikinsa. Ana budewa sai suka ga rauni a kirjinsa da kuma zuciyarsa, hakan ya sa suka yi gaggawar sanar da jami’an tsaro domin yin cikakken bincike.