✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda aka fara buga wasannin Gasar Zakarun Turai a yau

A daren yau [Talata] aka fara buga wasannin cin kofin Gasar Zakarun Turai na kakar wasannin bana 2022/2023. Za a buga wasannin ne da misalin…

A daren yau [Talata] aka fara buga wasannin cin kofin Gasar Zakarun Turai na kakar wasannin bana 2022/2023.

Za a buga wasannin ne da misalin karfe 7:45 na yamma, za a kuma a buga wasu da karfe 8:00 na daren yau Talata.

Ga rukunonin da kungiyoyin da za su buga gasar suke:
Rukunin E
Dinamo Zagreb
Chelsea
FC Salzburg
AC Milan
Rukunin F
Celtic
Real Madrid
RB Leipzig
Shakhtar Donetsk
Rukunin G
Borussia Dortmund
FC Copenhagen
Sevilla
Manchester City
Rukunin H
Benfica
Maccabi Haifa
Paris Saint-Germain
Juventus

Wasanni mafiya daukar hankali sune tsakanin PSG da Juventus,  da za a buga a filin Parc des Princes da ke kasar Faransa  da misalin karfe 8:00 na dare.

Akwai kuma wasan Sevilla da Manchester City ta kasar Ingila da za a buga a filin Estadio R. Sanchez Pizjuan da ke kasar Sifaniya, shi ma da misalin karfe 8:00 na dare.