Lamarin da ya fara shekaru biyu da suka gabata a matsayin soyayyar dandalin sa da zumunta na Instagram tsakanin matashi Suleiman Isah Isah na unguwar Panshekara a Jihar Kano da mayoyiyarsa, Janine Sanchezt ta birnin California na Amurka a karshe dai ya kai ga kulla auratayya.
Daurin auren dai ya gudana ne ranar Lahadi a Masallacin Barikin ’Yan Sanda da ke Panshekara a Karamar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano da misalin karfe 11:00 na safe.
- ‘Yadda auren dana zai kasance da matar sa Ba’amurikiya’
- Badakalar fansho: Maina ya sake sumewa a kotu
Mavauratan sun halarci wurin daurin auren nasu fuskokinsu cike da farin ciki suna masu samun fatan alheri daga dandazon mutanen da suka zo domin taya su murna.
Amarya Janine tare da ‘yan matan amarya a ranar daurin aure.
An kuma gudanar da daurin auren ne bisa tanade-tanaden addinin Musulunci.
Ango Suleiman dai ya biya amaryar sadaki N50,000 kamar yadda Shari’a ta yi tanadi.
Yayin daurin auren, tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani wanda dan uwa ne ga angon shi ne ya kasance waliyyin amarya.
Kazalika, amarya Janine ta kasance cikin shiga irinta Hausawa sanye da Leshi mai ruwan ganye da kuma lullubi a kanta.
Ta shaida wa Aminiya cewa farin cikinta ba zai misaltu ba.
Ta ce, “Za mu zauna a nan (Najeriya) na dan wani lokaci, daga bisani kuma zan wuce Amurka, shi kuma daga baya zai biyo ni da zarar ya sami bizarsa.”
Kawayen amarya zagaye da Janine a ranar yinin biki.
A nasa bangaren kuwa, ango Isah wanda aka fi sani da Babayaro ya ce ya cika burinsa a rayuwa.
“Gaskiya ba zan iya bayyana murnata ba a yau, kawai abin da zan iya cewa shi ne Alhamdulillah.
“Mutane da yawa sun dauka lamarin ba zai yiwu ba, sai ga shi yau Allah Ya yi.
“Ina kira ga samari kan duk wanda ya ga wata mace da yake so da kada ya ji komai, kawai ya tunkare ta, babu wata matsala,” inji angon.
Su kuwa iyayen angon, Malam Suleiman Isah da Malama Fatima Sulaiman, fatan alheri suka yi wa ma’auratan tare da cewa da yawunsu aka kulla auren.
Sun ce ko kadan ba su fuskanci wani kalubale ko tangarda daga ’yan uwa ba a kan lamarin.
Malama Fatima ta ce duk da yake angon shi ne danta na uku, amma ba ta taba yin bikin da ya tara jama’a kamar nasa ba.
Ta kuma ce ta gamsu da halayyar surukarta da kuma yadda take mu’amalantar jama’a ba tare da kyama ba.
Taron dai ya sami halartar dubban jama’a daga ciki da wajen jihar, ciki har da wani abokin angon a dandalin sa da zumunta na Facebook wanda ya taso kafa da kafa tun daga jihar Yobe domin shaida bikin.
Aminiya ta gano cewa amaryar, wacce ta kasance a birnin Kano kusan mako daya za ta kara wasu makonni biyun domin cin amarcinta kafin ta koma.
Ana sa ran angon, wanda yanzu haka yake aji biyu a Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano zai ci gaba da karatunsa a can Amurkan da zarar ya koma.