✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka ceto mata 4 masu ciki a gidan sayar da jarirai

Takaicin shi ne ta ci gaba da aikata laifin da ake tuhumar ta bayan kotu ta bada belinta.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta gano wani gidan da ake tsare ’yan mata ana yi masu ciki sannan kuma a sayar da jariran da suka haife.

Mai magana da yawun Rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya shaida wa Aminiya cewa sun ceto ’yan mata hudu masu juna biyu da yara hudu a gidan a ranar Talata 1 ga watan Disamba a yayin da suka kai simame gidan.

Ya ce hakan ya faru bayan da daya daga cikin matan da aka tsare a gidan wanda ke unguwar Ofada a yankin Mowe na Karamar Hukumar Obafemi-Owode, ta kubuce ana tsaka da yunkurin sayar da danta kuma ta shigar musu da korafi a kan lamarin.

DSP Abimbole ya ce sun cafke wata mata mai gidan sayar da jariran mai suna Florence Ogbonna, wacce a baya aka taba kama wa da laifin siyar da jarirai kuma aka gurfanar da ita a gaban kuliya.

Babban jami’in ya ci gaba da cewa, a wancan an kama matar ne da irin wannan laifi na tsare mata kuma ta sa a yi masu ciki daga bisani kuma ta sayar da jariran da suka haife.

“A wancan lokaci kotu ta bada belinta inda ake ci gaba da sauraron shari’ar lokaci zuwa lokaci.”

“Wani abun takaici shi ne, ta ci gaba da aikata laifin da ake tuhumar ta da shi bayan kotu ta bada belin ta, yanzu haka ta tsere a lokacin da jami’an ’yan sanda suka kai simame gidan, kuma jami’an suna kokarin ganin an sake shiga hannu.”

“Sai dai an yi nasarar cafke ’yarta da wani nakasasshen mutum wanda ta dauke shi aikin yi wa matan ciki idan sun haife sai ta sayar da jariran”, inji Abimbola.

Oyeyemi ya kara da cewa ’yan matan da suka ceto masu juna biyu ’yan tsakanin shekaru 18 zuwa 24 an kawo su jihar Ogun ne daga Jihohin Imo, Abiya, Akwa Ibom da Ebonyi.

Kazalika, ya ce akwai karin mata 6 da rundunar ta ceto wadanda basu kai ga daukar ciki ba doriya a kan hudun masu juna biyu.

Wasu daga cikin ’yan matan da ake ceto a gidan sayar da jariran sun shaida wa Aminiya cewa an yaudare su ne da zummar za a sama masu aikin yi, inda aka kawo su wajen matar ta tsare su ana kwanciya da su a yi masu ciki a sayar da jariran da suka haifa.

Cidere Onuoha, wadda ita ce matar da ta tsere daga gidan ta kuma shaida wa rundunar ’yan sanda halin da ake ciki, ta ce ana sayar da jarirai maza naira dubu 250 yayin da ake sayar jarirai mata naira dubu 200.