✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Tukur Mamu ya hana ceto fasinjojin jirgin kasa —Atta

Dan fasinjan da aka yi garkuwa da shi kuma mamba a kwamitin sulhu da ’yan bindiga ya zargi Tukur Mamu da manakisa da kuma ja…

Kwamitin Shugaban Kasa Kan Ceto Fasinjojin Jirgin Kasa daga hannun ’yan ta’adda, ya zargi masu shiga tsakani da yin zagon kasa ga kokarin gwamnati na ceto fasinjojin.

Mamba a kwamitin, Dokta Atta, ya zargi manyan masu shiga tsakani, ciki har da fitaccen dan jarida, Tukur Mamu, da yin duk abin da za su iya na hana gwamnati ceto mutanen saboda neman biyan bukantun kansu.

A cewar Atta wanda mahaifinsa ke cikin fasinjoijn da aka yi garkwua da su, da farko masu garkuwar ba su nemi kudi ba, Tukur Mamu ne ya shigar da maganar kudi, wanda ya kara dagula lamarin.

Ya ce, “Shigar da batun biyan kudi da Mamu ya yi ya sa iyalan mutanen da sace biyan sama da Dala 200,000, kafin Babban Hafsan Tsaron Najeriya ya shiga lamarin.”

Ya yi wannan zargi ne a lokacin da ake bayani kan yadda aka ceto mutanen, a hirar da aka yi da shi kai-tsaye a tashar talabijin na Channels.

Yadda aka ceto fasinojin jirign kasa

A cewarsa, “’Yan Kwamitin Shugaban Kasa sun sayar da ransu, saboda sai da muka shiga cikin dajin muka yi magana da ’yan ta’addan, har kwana mun yi a cikin dajin.”

A cewarsa, “Wata shida da mako guda ke nan, amma muna godiya ga Allah komai ya zo karshe.

“Muna kuma godiya ga Gwamnatin Tarayya da Babban Hafsan Tsaron Najeriya bisa taimakon da suka yi mana, har muka iya shiga cikin daji muka dawo da ’yan uwanmu da suka rage a hannun masu garkuwa da su.

“Wannan nasara da aka samu babu hannun wani mai cin amanar kwamitin da gwamnati, ina nufin Tukur Mamu, wanda ya yi duk abin da zai iya domin kawo cikas ga yunkurin gwamnati domin neman biyan bukatar kansa.

“Sanin kowa ne cewa yanzu yana tsare a hannun gwamanti, amma muna godiya ga Allah, ’yan uwanmu sun dawo baki dayansu.

“’Yan bindigar ba su nemi kudi ba da farko, shi ne ya shigo da maganar kudi, wanda da hakan ya sauya akalar maganar, har mutanen suka kai wata shida a daji; Mun kuma yi asarar kimanin Dala 200,000 saboda wannan.

“Mun gode Allah Babban Hafsan saron Najeria da a shiga lamarin a kafa  kwamiin da bai nemi ko kobo ba.

“Duk wani kokari da aka yi na kashin kai ne domin tabbatar da ganin an sako mutanen da aka i garkuwa da su.

“Ina tabbatar muku cewa a cikin kwamitin na yi aiki da mutane masu matukar nagarta da rikon amana.

“Da ina da hali da kowannensu sai an ba shi lambar girmamawa ta kasa saboda yadda suka sadaukar da rayukansu, suka shiga daji suka kwana.

“Mun saurari korafin wadanan mutanen (’yan ta’addan), duk da cewa an san abin da suka aikata ba daidai ba ne, amma duk da haka mun tatttauna da su.

“Abin da ya kamata a yi nan gaba, shi ne hukumomin tsaro su rika hadin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu sannan gwamnati ta kara bayar da damar ci gaba da tattaunawa.”

Biyu daga cikin fasinjojin jirin kasan sanye da kayan asibiti mai launin ruwan kasa tare da ’yan uwansu a Asitin Rundunar Sojin Sama da ke Kaduna. (Hoto: Maryam Ahmadu Suka).
%d bloggers like this: