Bayanai sun nuna yadda aka yi ta kai ruwa rana kafin a kai ga ceto daliban Makarantar Sakadaren GSS Kankara, Jihar Katsina, kwana shida bayan ’yan bindiga sun sace su daga makarantar.
An karbo dalibai 344 da maharan da suka yi musayar wuta da jami’an tsaron da ke gadin GSSS Kankara suka yi awon gaba da su ne bayan kwana shida a hnnun ’yan bindigar.
- Daliban Kankara na hanyar komawa gida —Gwamnatin Katsina
- An gano Daliban Kankara a dajin Zamfara
- Gwamnatin Katsina ta karyata labarin sako Dalilan Kankara
- Aisha Buhari ba ta ce komai kan Daliban Kanakara ba
Gwamnatin Jihar Katsina, ce ta tabbatar a daren Juma’a cewa masu garkuwar sun saki yaran a garin Tsafe, Jihar Zamfara mai makwabtaka da jihar.
Gwamna Aminu Bello Masari ya ce an ceto yaran ne ba tare da biyan ko sisi na kudin fansa ba.
Gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce sulhu aka yi aka da ’yan bindigar kafin a kai ga karbo yaran su 344 ba tare da an dauki tsawon lokaci ba.
Matawalle ya ce a hannun Fulani ’yan bindiga aka karbo yaran ba a hannun kungiyar Boko Haram ba.
Sakataren Sakataren Gwamnatin Jihar, Bala Bello Maru ya ce babu ko daya daga cikin daliban da aka sako da ke rashin lafiya ko ya samu matsala.
Sojoji ne dai suka karbo yaran suka fito da su daga cikin dajin Tsafe a Jihar Zamfara, suka mika su ga tawagar Gwamnatin Zamfara da magaribar ranar Alhamis.
Daga Gusau kuma aka garzaya da daliban zuwa barikin sojoji da ke Gusau, hedikwatar Jihar kafin daga bisani a karasa da su Katsina.
Sai dai majiyarmu ta ce bayan masu garkuwar sun ki amincewa da da jami’an tsaro a tattaunawar, sai gwamnati ta shigar da masu rike da sarautun gargajiya, yawancinsu, na Fulani domin sasantawar.
Majiyarmu ta ce a lokacin da suke cikin daji, yaran an raba su ne gida uku inda gungu uku kowanne yana tare tsare da kashi daya a wurare daban-daban.
Ta ce bayan an gama sasantawa masu garkuwar garkuwar sun mika yaran ga masu unguwanni a rukuni rukuni.
Bayan cimma yarjejeniyar, an fara kai yaran da aka saki ne zuwa kauyen Hayin Alhaji a cikin Ardo motoci kirar Hilux.
“Dag Hayin Alhaji, sai aka kai su kauyen ’Yan Warin Daji, inda aka mika su ga jami’an tsaro,” inji majiyar.
Mazauna sun ce sun ga jami’an tsaro, wasunsu a cikin farin kaya, suna ta kai-komo a yankin a lokacin da ake komawa da yaran.
An kuma ga helikwafta na zarya a yankin Dajin Rugu, wanda ya keta kananan hukumomi da dama a jihohin Zamfara, Katsina kuma Kaduna.
Yadda aka yi sulhu
Gwamnatin Zamfara ta ce bayan shiga tsakanin da Gwamna Bello Matawalle ya yi da masu garkuwar ne aka karbo su.
Ta ce Sakataren Gwamnatinta, Bala Bello Maru, ne ya jagoranci karbo su, kuma suna koshin lafiya a lokacin da suka isa birnin Gusau.
Ya ce daukacin daliban da aka sako suna cikin rashin lafiya kuma babu ko daya daga cikinsu da ya samu matsala.
Da yake bayani, Gwamna Matawalle na Zamfara ya ce gabanin cimma daidaito Fulanin sun turje, amma daga bayya Allah Ya taimaka a aka shawo kansu suka amince su sako yaran.
“An yi zaman sulhu akalla sau uku kafin a kai ga cimma daidaito ga sakin daliban, da farko ya ci tura, haka zama na biyu amma a ƙarshe an yi nasara.”
Majiyarmu ta ce sulhun ya kuma kunshi tattaunawa da masu rike da sarautar gargajiya, har ta kai ga an sako yaran.
Bukatun masu garkuwar da Daliban Kankara
Ya ce a lokacin tattaunawar sulhun, Fulanin da suka yi garkuwa da daliban sun lissafo wasu matsaloli wadanda aka yi musu alkawari za a sasanta.
Ya ce Fulanin sun nemi a tabbatar da cewa jamian tsaron sa-kai, ’yan mato da gora da ’yan banga sun daina cin zarafinsu ko kashe musu shanu.
Gwamnan ya ce a shirye yake a ci gaba da irin wannan wajen sulhu don tsare kasa, kuma duk wanda ya ki zai fuskanci fushin hukuma.
Labarin karbo daliban daga hannun Fulani ’yan bindiga ya sanya farin ciki a zukatan al’umma.
Sai dai wasu na diga alamar tambaya a kan bidiyo da kungiyar Boko Haram ta fitar, wanda ciki Shugabanta, Abubakar Shekau ke ikirarin garkuwa da daliban.
Bayan Gwamnatin Katsina da Rundunar Tsaro ta Najeriya sun karyata bidiyon, inda rundunar ta ce farfaganda ce kungiyar ke yi.
Na nashi bangaren, Gwamnan Katsina, Aminu Masarai, ya ce an gano cewa yaran suna cikin daji a Jihar Zamfara, kuma ana tattaunawa da masu garkuwa da su wadanda ya ce ba Boko Haram ba ne.
Sai dai a bidiyo na biyu da aka saki ’yan sa’o’i kafin a karbo yaran, wani yaro ya yi bayani a madadin sauran, yana rokon gwamnati ta cece su ta kuma biya bukatun maharan.
An kuma ji muryar wani mutum yana magana da muryar Bafulatani yana fadin bukatunsu, dalibin na maimatawa.
Bukatun masu garkuwar sun gauraya tsakanin wadanda ake ganin na Bok Haram ne da kuma wadanda na ’yan bindiga ne.
“Muna kira ga gwamnati da ta rushe duk wani rukunin masu aikin sa-kai na kato da gora, a rufe kowace irin makaranta sai dai ta Islamiyya.
“A mayar da dukkan sojojin da aka turo nan saboda babu abin da za su iya yi musu wallahi. Jiragen nan ma a daina turowa. A taimaka mana daga halin da muke ciki,” inji yaron.
Ya kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da ta daidaita da masu garkuwar, tare da gargadin kada ta yi amfani da karfin soji wajen kubutar da su.
Tsakanin Boko Haram da ’yan bindiga
Hakan ta sanya wasu ke tunanin ko Boko Haram ta fara amfani ko hada baki da ’yan bindiga yankin Arewa maso Yamma ne.
Wasu kuma na ganin wani sabon salo ne da ’yan bindigar suka fito da shi na sakin bidiyo.
Tun da farko dai wasu masu sharhi sun nuna shakkunsu kan bidiyon farko da aka fitar.
Sun ce wanda ya yi magana a matsayin Shugaba Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi inda-inda wurin kiran sunan kungiyar: Jama’atu Alhis Sunnah Lidda’awati Wal Jihad.
Ya kuma kira sunansa Abubakar Shekau, sabanin yadda yake ce wa kansa, Abu Muhammad Asshakawi.
Amma sun ce, in banda wadannan abubuwa, sakon na Boko Haram ne.
Kudin fansa
Babu wani bayani da aka samu da ke tabbatar da cewa an biya kudin fansa ga ’yan bindigar.
Amma wasu na ganin abu ne mai matukar wuya a ce an sako yaran ba tare da an biya kudin fansa ba.
A lokacin da aka karbo ’yan matan Chibok da ’yan matan Dapchi da Boko Haram suka yi garkuwa da su, sai da aka biya kudin fansa.
A wani lokaci ma har da sakin mayakan kungiyar da ke hannun gwamnati.
Sai dai a baya-bayan nan gwamnatin kan yi dari-dai wurin yin bayani ko goyon bayan a biya masu garkuwa da mutane kudin fansa.