An ceto hakimin kauyen Garin Babba da ke Karamar Hukumar Garun Mallam ta Jihar Kano, Abdulmuminu Mudi daga hannun ’yan bindiga.
Hadin gwiwar ’yan sanda da ’yan banga ne suka ceto basaraken bayan ’yan bindiga sun kai hari a kauyen da talatainin daren ranar Talata suka yi awon gaba da shi.
Wani mamba a kwamitin tsaro na Garun Malam, Aminu Garba Ali ya ce, “Sun zo da misalin karfe 3:30 na safe ne suka yi kokarin daukar hakimin kauyen.
“Sun kasa tafiya tare da shi ba saboda ’yan banga sun dakile yunkurin, suka ceto shi tare da kwato babura uku.”
Da yake tabbatar da hakan, Kakakin ’yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce an yi nasarar kubutar da basaraken kauyen ne bayan samu rahoton cewa ’yan bindiga a bisa babura sun yi garkuwa da shi.
Bayan nan ne hadakar ’yan sandan daga Garum Mallam da rundumarsu mai yaki da masu garkuwa da mutane da ’yan banga na yankin suka kai dauki domin ceto shi.
Ya ce masu garkuwa da mutanen sun yi watsi da basaraken da babura uku, inda ya kara da cewa an ceto hakimin ba tare da jin rauni ba, sannan aka kwato baburan.