Matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta ce jirgin Sojin Sama da ya dauko ta bayan ta baro asibiti zuwa Najeriya “ya sama tangarda saboda iska mai karfi a sararin samaniya”.
Ta ce, “amma matukin jirgin da ‘yan tawagar sun shawo kan matsalar cikin kwarewa”, a hanyar tasu ta dawowa daga birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Ta yaba da jarumta kuma kwarewar da tawar suka nuna, tama mai jinjina ga “zaratan dakarun Rundunar Sojin Sama ta Najeriya maza da mata” bisa sadaukar da kansu wajen aiki da kula da jirage.
Bayan dawowarta gida a ranar Asabar, a sakon da tafitar, Aisha Buhari ta yi godiya ga ‘yan Najeriya da suka yi mata addu’o’i a lokacin da ta tafi duba lafiyarta.
“Yanzu na warke, na murmure kuma na dawo gida Najeriya”, inji ta.
‘Jirgin Aisha Buhari saura kiris…’
Wasu kafafen labarai (ba Aminiya ba) sun ruwaitowa cewa saura kiris da an yi rashi, bayan jirgin da ya dauko Matar Shugaban Kasar da diyarta Hanan, wadda za a yi bikinta a ranar 4 ga watan Satumba, ya kwace na kusan minti 10 bayan tafiyar sa’a biyar a sararin samaniya.
Sai dai tun kafin fitar sakon na matar Shugaban Kasar, majiyarmu a Fadar Shugaban Kasa ta yi watsi da labarin, inda ta yi bayanin cewa abin da ya faru ba bako ba ne ga jiragen sama.
Majiyar ta ce gargada ce ta jiragen sama ke fuskanta a sararin samaniya sakamakon haduwa da iska mai karfi.
Tun baya Babbar Sallah ne Aisha Buhari a tafi asibiti a UAE, wanda wasu rahotanni ke cewa ta yi ta fama da rashin lafiya.
Kafin tafiyar tata dai an gan ta ta halarci Sallar Idi a Fadar Shugaban Kasa, cikin kiyaye matakan kariyar cutar COVID-19.
Bayan Sallar Idin kuma an ga ta dauki hotuna tare da iyalanta a Fadar Shugaban Kasa.