✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Abiola Ajimobi ya rasu

Abiola Ajimobi tsohon Gwamnan Jihar Oyo ya rasu ne bayan sassan jikinsa da dama sun daina aiki sakamakon kamuwarsa da cutar COVID-19. Gwamnatin Jihar Legas…

Abiola Ajimobi tsohon Gwamnan Jihar Oyo ya rasu ne bayan sassan jikinsa da dama sun daina aiki sakamakon kamuwarsa da cutar COVID-19.

Gwamnatin Jihar Legas inda Ajimobi ya rasu, ta ce sassan jikin nasa sun bar aiki ne bayan tsananin da cutar ta COVID-19 ta yi a jikinsa.

Sanarwar da Kwamishinan Lafiya na Jihar Legas Farfesa Akin Abayomi, ya fitar a safiyar Juma’a ta ce ajalin tsohon gwamnan ya cika ne a Asibitin First Cardiologist Consultant, daya daga cikin cibiyoyin kula da masu cutar coronavirus masu zaman kansu a jihar Legas. Ya kuma mika ta’aziyya ga iyalai da masoyan mamacin musamman jama’ar Jihar Oyo.

A ranar Alhamis 25 ga watan Yuni 2020, Allah Ya yi wa marigayin rasuwa yana da shekaru 70 bayan fama da rashin lafiya.

Ta’aziyyar rasuwarsa
Tun bayan rasuwarsa jama’a ke ta tururuwa domin ta’aziyyar da juyarin rasuwar fitaccen dan siyasar kuma tsohon dan majalisar tarayya, baya ga wadanda ke ta aika sakonnin ta’aziyya tare da yaba kyawawan halayen mamacin.
Wasu wadanda suka yi sammakon zuwa ta’aziyya a gidansa a Ibadan, Jihar Oyo
Takaitaccen tarihinsa

Aminiya ta kuma yi muku talhisin takaitaccem taro da wasu muhimman abubuwa game da shi:

 

Tasowarsa

  • An haifi Abiola Ajimobi ranar 16 ga watan Disambar 1949 a Oja-Iba, da ke Ibadan, Jihar Oyo.
  • Ya yi karatun Firamare a Saint Patricks, da ke Oke-Padre a Ibadan.
  • Ajimobi ya kasance mai shiga harkokin wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ciki har da kwallon kafa inda ya zama mai jagorantar harkar wasanni a makarantar sakandaren da ya halarta.

Karatunsa 

Marigayi Ajimobi ya karanta Harkokin Tafiyar da Kasuwanci da Kudade a Jami’ar Jihar New York da ke a Buffalo a kasar Amurka – inda ya samu shaidar digrinsa na farko.

Sannan ya yi digiri na biyu a bangaren Nazarin Kasuwanci da Kudade a wata Jami’a mai suna Governors State University da ke Illinois a Amurkar.

Iyalansa

  • Ya auri uwargidarsa Misis Florence Ajimobi a shekarar 1980 inda suka haifi ‘ya’ya biyar.
  • ‘Yarsu ta fari, mai suna Abisola Kola-Daisi ta kasance mai hazakar harkar kasuwanci ta mallaki wani katafaren shago mai suna Florence H Luxury.
  • Shi ne mahaifin mijin diyar Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje , wata Fatima.

Siyasa

  • A shekarar 2003, Ajimobi ya zama dan majalisar dattawa daga jiharsa ta Oyo. Ya zama Mataimakin Shugaban Marasa rinjaye a zauren.
  • A shekarar 2007 ya yi takarar gwamna karkashin jam’iyyar ANPP, amma bai yi nasara ba a lokacin.
  • Sai dai ya sake gwada sa’arsa a shekarar 2011 karkashin jam’iyyar ACN inda ya yi nasarar darewa kujerar gwamnan jihar Oyo.
  • Ya sake neman wa’adi na biyu a zaben shekarar 2015, a karkashin jam’iyyar APC; inda ya fafata da tsoffin gwamnonin jihar biyu da suka rike mukamin gabanin sa, wato Christopher Alao Akala da Rashidi Adewolu Ladoja.
  • Da ya yi nasar da shi ne zai fara zama gwamna da ya taba yin tazarce zuwa wa’adi na biyu a jere a tarihin Jihar Oyo.
  • An zabe shi a matsayin Sanata karkashin jam’iyyar APC daga mazabar Oyo ta Kudu a ranar 28 ga watan Satumban 2018.
  • A ranar 9 ga watan Maris, 2019, Ajimobi ya sha kaye – a yunkurinsa na neman zarcewa kan kujerar, a hannun dan takarar jam’iyyar PDP Kola Balogun.
  • A ranar 17 ga watan Yunin da muke ciki ne Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar APC ya sahale masa da ya zama shugaban riko na jam’iyyar na kasa.

Karshen rayuwarsa

A ranar 18 ga watan Yunin an yi ta yada jita-jitar cewa Ajimobin ya rasu; amma daga bisani aka gano cewa karya ce.

A ranar Alhamis 25 ga watan Yuni 2020 ya rasu bayan ya yi fama da rashin lafiya mai tsanani.

Yadda ya bar duniya

Ajimobi ya rasu yana da shekara 70, a asibitin First Cardiology Hospital, Ikoyi a jihar Legas, inda aka yi jinyar tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Malam Abba Kyari, wanda shi ma cutar coronavirus ta kashe.

Rasuwar tasa na zuwa ne bayan a makon jiya an yi ta baza jita-jitar ya rasu kafin daga bisani iyalai da makusantansa su karyata rade-radin.

Wasu majiyoyi na cewa Ajimobi ya shafe mako guda yana halin rai kwakwai mutu kwakwai kafin kafin daga bisani rai ya yi halinsa.

Kafin rasuwarsa, Ajimobi shi ne wanda Kwamitin Gudanarwa (NWC) na Jam’iyyar APC ya nada shugabanta na riko, amma rashin lafiyar ta sa aka nada Hilliard Eta mukaddashinsa.

Kafin nadin, shi ne Mataimakin Shugaban Jam’iyyar (Kudu-maso-Yamma), kuma ya yi Dan Majalisar Dattawa daga Jihar Oyo.