✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Abacha ya yaudari ’yan Najeriya ya hau mulki —IBB

Gwamnatin Abacha tana da wayo, sun san wadanda suka fi magana a kan zabe da juyin mulki.

Tsohon Shugaban Najeriya a zamanin mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya sanar cewa takwaransa wanda ya mulki kasar daga shekerar 1993 har zuwa mutuwarsa a 1998, marigayi Sani Abacha, ya hau mulkin ne bayan ya yaudari wasu masu gwagwarmaya da masu fada a ji da sauran manyan ’yan siyasa na kasar.

Tsohon Shugaban wanda ake yi wa lakani da IBB, ya bayyana haka ne a hirarsa da Trust TV,  yayin da yake bayyana yadda Abacha ya yi yaudari mutane ya kwace mulki.

Babangida ya ce, “gwamnatin Abacha tana da wayo. Sun san wadanda suka fi magana a kan zabe da juyin mulkin da batun 12 ga watan Yuni da sauran abubuwa.

“Sai suka fara magana da su, suka yaudare su da karfafa musu gwiwa su kawar da gwamnatin rikon-kwarya, da cewar idan sun kawar da gwamnatin rikon-kwaryar, za su dawo da su, su ba su abin da suke so mulkin dumokuradiyya, daga nan sai a kafa gwamnatin farar hula.

“Da wannan suka yaudari jama’a da sauran fitattun mutane, saboda haka da Abacha ya shigo, sai ake ta murna, hankali ya kwanta; Madalla abu ya yi kyau! Abin da zai faru a gaba kuma shi ne zababbiyar gwamnatin dumokuradiyya.

“Ni na sani, mun sani, hakan ba zai yiwu ba saboda maganar ita ce: (Abacha zai ce ), Me zai sa in sa kaina cikin hadari, kawai in zo in danka muku mulki? Wannan shi ne abin da ya faru,” inji Babangida.

Abacha, wanda IBB ya bayyana a matsayin babban abokinsa, ya kasance hafsan hafsoshin sojoji a lokacin mulkin Babangida daga 1985, kuma daga baya ya nada shi Ministan Tsaro a 1990.

Cikin wata sanarwa da ta karade kusan ko’ina a ranar 17 ga watan Nuwamban 1993, aka bayyana cewa Abacha ya karbe mulki daga hannun tsohon shugaban kasa, Ernest Shonekan, kan abin da suka bayyana a matsayin dalilai na rashin tabbas da suka shafi siyasa da zamantakewar al’umma.

%d bloggers like this: