✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Abacha da Abiola suka rasu a hannuna –Farfesa Sadik Wali

Farfesa Sadik Suleaiman Wali, babban likita ne da ya yi aiki a fadar shugaban kasa, inda ya duba lafiyar  shugabannin kasar nan biyar da suka…

Farfesa Sadik Wali a lokacin tattaunawarsa da wakilanmuFarfesa Sadik Suleaiman Wali, babban likita ne da ya yi aiki a fadar shugaban kasa, inda ya duba lafiyar  shugabannin kasar nan biyar da suka hada da Janar Muhammadu Buhari da Janar Ibrahim Babangida da Cif Ernest Shonekan da marigayi Janar Sani Abacha da kuma Janar Abdulsalami Abubakar. A wannan tattaunawa ya tabo batutuwa da dama da suka hada da yadda Janar Abacha da Cif MKO Abiola suka rasu:

Jama’a za su rika tuna ka a matsayin babban likita ga tsofaffin shugabannin kasar nan biyar. Mene ne labarinka? Kuma yaya aka yi ka samu wannan mukami?
Lamari ne mai ban sha’awa. Ban yi tsammanin faruwar haka ba. Bayan kammala jami’a na tafi Ingila na yi karatu inda na zama kwararren likita. Sai na dawo Jihar Kano na yi aiki na kamar shekara uku. To na fi son aikin koyarwa don haka na tafi Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya. Ina can lokacin da Shugaban kasa Shehu Shagari ya nemi in zama likitansa, amma na nuna rashin sha’awa. Lokacin ni matashi ne kuma ban dade da fara aikin koyarwa ba. Don haka sai na ki karba. Wani abin sha’awa a daidai lokacin sai Jihar Kano ta ba ni, ko in ce ta tilasta in zo in zama Kwamishinan Lafiya. To, yadda aka yi ke nan na zama Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano, a maimakon zama likitan Shugaba Shagari.
…wannan ya kasance lokacin mulkin marigayi Abubakar Rimi ke nan
Eh, na yi Kwamishinan Lafiya lokacin mulkin Gwamna Abubakar Rimi ne. Shugaba Shagari kuma ya dauki Dokta dalhatu Sarki Tafida. Dokta Tafida kuma ajinmu daya, yadda lamarin ya faru ke nan. Abu ne mai wahala in bayyana ga yadda aka nada ni likittan Shugaban kasa. Ina jin mukamin ne ke bibiyata. Domin Janar Muhammadu Buhari wanda ya hau mulki a 1984 ne ya nemi in zama likitansa.
A lokacin na san shi sosai, saboda muna tare a Legas lokacin da aka yi juyin mulkin Janairun 1966. Su Murtala da Gowon da Buhari… Duk suna nan kuma wannan ne ya sa muka san juna. Don haka lokacin da ya ce, in zama likitansa na ga ya dace in yi hakan. Kuma ba wannan kadai ba, ni ma soja ne. Ka san a lokacin Yakin Basasa ana tura likitoci su shiga soja. Kusan an tilasta mu ne, duk da dai mun ji dadi.
To ina aikin soja aka tura ni Awka, birged din da Janar Buhari yake. Na yi sha’awar dabi’arsa, amanarsa da gaskiyarsa. Don haka lokacin da ya zama Shugaban kasa kuma ya bukaci aiki da ni, na amince. Yadda lamarin ya fara ke nan.   
Bayan shekara daya da rabi sai aka yi juyin mulki. Ba na kasarnan a lokacin. Ina Amurka tare da iyalinsa (Buhari) – matarsa da dukkan ’ya’yansa. Lokacin da muka dawo sai na je na samu Shugaba Janar Ibrahim Babangida na ce “Na dauki hutu na shekara biyu ne daga jami’a. Kuma duk da shekara biyun ba ta cika ba, zan koma.” Amma ya ce a’a ba zan koma ba, wannan shi ne abin da ya faru. Hakika na so komawa jami’a, amma ya ki. Sai na zauna a can, shi kuma ya dade yana mulki. Bayansa sai Cif Ernest Shonekan. Na yi aiki da shi na ’yan watanni. Bayan Shonekan sai Janar Sani Abacha ya zo, kuma wannan ne lokaci mafi kalubale. Na fada wa kowannensu cewa ina son tafiya, amma suka rika rokona in zauna. Yadda aka yi na zauna dogon lokaci ke nan.
Ka ce, lokacin Janar Abacha ne ya fi zama kalubale, me ya sa hakan?
Lokacin mulkin Abacha da rasuwarsa babban kalubale ne, saboda ban taba gani ba, kuma tun daga lokacin ban kuma sake ganin damuwa irin wannan a rayuwata ba. Kai ne likitan mutum kuma a ce kusan ya rasu ne a hannunka. Wannan shi ne abin da ya faru, amma abu ne mai ban mamaki. Yana da matsalolin rashin lafiya, amma an shawo kansu. Ya warke sarai kuma yana cike da kazar-kazar.
Kwana daya kafin ya rasu ya je ya ga tashin shugaban Falasdinawa na lokacin Yasser Arafat a filin jirgin saman Abuja. Bayan haka muka dawo gida muka yi ban kwana da juna, ya hau sama duk muka watse, sai a ranar 8 ga Yuni wajen karfe 6:00 na safe Babban Jami’in Tsaro, Manjo Hamza Al Mustapha ya bugo min waya ya ce, “Ka zo, aikin gaggawa ya taso.” Kaina ya daure, me ya faru. Ina cikin kintsawa ina kokarin in nemo direba ya kai ni can, kwatsam sai na ga wasu mutane sun zo. Ya aiko mutane daga bangaren tsaro su dauke ni. A lokacin ne na san wani al’amari marar dadi ya faru. Kuma a lokacin da nake shiga Fadar Shugaban kasa akwai kofar da mutane ba sa shiga, Shugaban kasa ne kawai ke amfani da ita. Sun bude ta; ba su gaya min abin da ya faru ba. Sai muka shige ciki, muka iske shi rashin lafiyarsa ta tsananta…  
…Ke nan bai rasu ba a lokacin?    
Kusan ya rasu, yana ta fitar da kumfa daga bakinsa… Muka yi abin da za mu iya domin farfado da shi, baya ga haka babu wani abu da za mu iya.
Su wane ne suke tare da ku a lokacin?
Manjo Al-Mustapha yana wurin da wasu jami’an tsaro da masu aikin gida da wani Dokta Maina wani likitan tiyata. Yana wurin. Wadannan su ne mutanen da suke kewaye da shi; lokacin da muka yi kokarin farfado da shi muka yanke kauna sai na je na gaya musu…
Me ya jawo rasuwarsa?
Bisa ga aikin likita, bugawar zuciya ce. Gaskiya babu wani a cikinmu da zai iya gaskata hakan. Don haka a matsayina na likita sai na kira wanda ya fi kusanci da shi. Don haka na kira dansa da dan uwansa. Yana da dan uwa Manjo Abdulkadir Abacha a cikin fadar da kuma dansa Mohammed Abacha. Muka kira su muka ba su labarin. Abu ne mai matukar bakanta rai.

Lokacin da kuke kokarin farfado da shi, ba su san abin da ke faruwa ba ne?  
Ba su sani ba, rana ce kamar kowacce, suna barci. Sai muka buga musu kofa muka tashe su. Lokacin da suka fito, sai na shaida musu abin da ya faru. Kamar yadda kowa zai zata, sai suka kama kuka. Sai da na rika ba su baki, sannan na ce, “Wane mataki na gaba kuke so mu dauka?”
Suka ce abin da ya fi dacewa a kira  Mashawarcin Shugaban kasa kan Harkokin Tsaro (NSA), Isma’ila Gwarzo, saboda wannan batu ne na tsaro. Sai aka kira NSA, kuma a yayin da muke kintsa gawarsa, shi kuma yana magana da ’ya’yansa da Manjo Al-Mustapha kan abin da za a yi.
 An yi gwaji kan gawar?
Na ce a yi gwaji kan gawar, kuma na tuna na ce da Ibrahim Coomassie (Sufeto Janar na ’Yan sanda a lokacin) a yi gwaji kan gawar. Ina jin daya daga cikin ’ya’yansa ya goyi bayana, amma sai ya hau sama ya ga mahaifiyarsu. Suka tattauna a kai ya dawo ya ce, ba su bukatar yin gwaji a kan gawar… Amma na dauki samfurin jininsa don nazari, kuma ya nuna cewa bugun zuciya ne.
A nan ya kamata a tsaya?
Ba a nan ba ne, inda ya kamata a tsaya shi ne wanda ya kamata a yi. A aikin likita, bugawar zuciya ce, kuma gwajin likita ya karfafa hakan. Amma nazari na karshe zai samu ne ta yin gwaji kan gawar, kamar yadda muka yi kan gawar Cif MKO Abiola domin ganin hakikanin abin da ya faru.
Fitar kumfar na da alaka da cin tuffa ne, saboda akwai jita-jitar cewa wasu ’yan matan Indiya sun ba shi tuffa mai guba ya ci, ya rasu?
(Girgiza kai). A’a. A’a, ba haka ba ne. Wannan daya ne daga cikin karairayin da wasu mutane suka kirkiro. A matsayina na likita, ina tabbatar maka ya rasu ne sakamakon bugun zuciya, ko abin da muke kira ciwon zuciya.
Kamar yadda na ce, lokacin da na gan shi a wannan mummunan hali na kira wasu likitoci su zo su taimaka mu gani ko za mu iya farfado da shi. Babu wani batun guba a cikin tuffa.
Mu koma baya kadan kan Janar Buhari. Kai makusancin iyalinsa ne lokacin yana Shugaban kasa. Shin yana da matsalar rashin lafiya ce ko iyalinsa?
Yana da ’ya mai ciwon sikila wato Zulaiha wadda ta rasu kwanakin baya. Wannan ne babbar matsalar lafiyar. Amma shi lafiyayyen mutum ne. Mattarsa ma lafiyayyiya ce. Zulaiha ce take sa mu shiga da fita. Mun je Jamus da ita, mun je Amurka; da asibitin soja a can. Ina tare da ita da matarsa lokacin da juyin mulkin ya auku. Shi ya sa na ce, abu ne mai matukar daga hankali.
Kana aiki a Fadar Shugaban kasa lokaci da Cif Abiola ya rasu. Ko za ka iya ba mu haske a kai?
Na san Cif MKO Abiola sosai. Har ma yana ziyartata a gidana na Legas da ke Glober Abenue a Ikoyi.  Lokacin da yake shirye-shiryen fitowa takarar Shugaban kasa, duk lokacin da ya je ganin Shugaba Babangida nakan yi wasa da shi, nakan ce masa cikin raha, “bari in auna hawan jininka. Domin ba ka barci.” Muna dasawa sosai, na san wasu daga cikin matsalolinsa. Yana da hawan jinni. Kuma na gaya masa ya kwatar da hankalinsa ya rika barci sosai. Wannan shi ne halin da yake ciki. Ba na kasar nan, sai a daren da zai rasu na dawo, saboda na dauki hutu na fita waje da iyalinsa na tsawon mako uku. Amma sai na ce zan dawo kafin cikar lokacin. Don haka na dawo ranar Litinin da dare, ranar Talata da safe na tafi aiki, kuma ina ofis misalign karfe 12:00 na rana na samu waya daga Babban Jami’in Tsaron Shugaban kasa (CSO) Manjo Abdulrashid Aliyu.
Ya kira ni ya ce, in zo Aguda House kan wani abu na gaggawa. Na tambayi kaina “wane abu ne na gaggawa haka?” Sai na ce, “bari in je gida in dauko wasu kayan aikin likitana,” saboda a lokacin ina ofis a Fadar Shugaban kasa, ba ina asibitin Fadar Shugaban kasa ba ne. A kan hanyata, sai na hadu da shi, sai ya ce, “A’a, likita, dawo mu tafi Aguda House kai-tsaye.” Sai muka juya zuwa Aguda House, na tuna nag a Cif Abiola. Yana sanye da fararen tufafi, tufar da ya fi so, wato leshi. Ina jin an ce akwai yiwuwar a sake shi washegari. Wannan shi ne abin da ake ciki.  To lokacin da na shiga ciki, na iske wasu Amurkawa biyu a can, Susan Raice da Thomas Pickering, sannan akwai wasu jami’an tsaro da ma’aikatan gidan duk suna nan, sai na gan bakinsa na ta kumfa…
Shi ma ya rasu irin yadda Abacha ya rasu?
Gaskiya ya yi kama sosai. Sun ce ya sha shayi ke nan… Bayan shan shayi ya shiga ban-daki bai dawo da wuri ba. Daga baya ya fito ko suka fito da shi. Amma na iske shi bakinsa na fitar da kumfa, sai muka fara aikin farfado da shi. Gaskiya bai mutu ba a lokacin. Daga nan sai na sanar da abokan aikina a Fadar Shugaban kasa cewa su shirya muna da wani aikin gaggawa. Sai muka garzaya da shi cikin mota, ba ta daukar marasa lafiya ba, daga Aguda House zuwa Asibitin Fadar Shugaban kasa. A nan ma Susan Rice da Pickering suka biyo mu can. Muka sake yin duk abin da za mu iya don farfado da zuciyarsa ta yi aiki, amma ba mu samu nasara ba.  
Dukkan likitocin suna nan, muna da masu aikin fida da sauran likitoci, muka sanya wasu abubuwa a cikin zuciyarsa muka yi kokarin farfado da shi; amma bai yiwu ba. Bayan wani lokaci da na lura da matsalar, wasu ma’aikatan suka ga munin matsalar. To a fili ne mutane suka ga Cif Abiola ne, idan batun ya fito fili na iya jawo mummunan hautsini a kasar nan. Don haka nan da nan, sai na ba da shawarar abin da za a yi a sanar ta kafafen watsa labarai kafin mu fara jin jita-jita a gefe.  Wannan mataki yana da matukar muhimmanci a lokacin. Zuwa lokacin sai daya daga cikin matan Abiola da ’yarsa da suka zo Abuja domin su gan shi daga farko, suna filin jirgin sama. Sun zo Abuja sun gan shi yini daya kafin nan, suna kan hanyarsu ta komawa Legas. Sun zauna tare da Babagana Kingibe. Suna filin jirgin saman, sai muka kira Kingibe muka shaida masa cewa iyalan su dawo. Suka dawo ba su san abin da ya faru ba. Muka aika da sako ga Shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar a lokacin suna gudanar da taron Majalisar Gudanarwa ta Mulkin Soja, (AFRC) muna sanar da shi abin da ya faru.
An bayar da sanarwa nan da nan?
Eh, an sanar a labaran karfe shida. Ban ji ba, amma na san an yi. Saboda a cikin asibitin akwai mutane da dama da suka ce sun ji, kuma saboda ya riga ya rasu, babu abin da za ka boye.
Labarin zai fito fili, kuma za a samu mummunan tashin hankali. Don haka abu na gaba da za a yi shi ne a sanar da iyalinsa, wanda shi ma abu ne mai wahala.
Kamar yadda na sanar da rasuwar Janar Abacha ga dansa da dan uwansa, haka dole zan sanar da iyalan Abiola. Janar Abdulsalami Abubakar da wakilan AFRC suka zo na yi musu bayani.
Yaya Shugaban kasa ya karbi labarin?
To, ka san sojoji, za su kadu, amma suna natse, kuma ina jin Shugaban kasa ya riga ya ji labarin. Jami’an tsaro sun riga sun gaya masa. Ba ni na gaya musu ba, amma na gana da su na yi musu bayani lokacin da suka fito daga cikin taro.
Zuwa lokacin an dauki matar Abiola da ’yarsa daga filin jirgin sama zuwa gidan Janar Abdulsalami. Kuma a lokacin ba a gaya musu abin da ya faru ba. Suna dai zaune ne kawai a gidan. Lokacin da na gan su, sai suka ce in ba su labarin abin da ake ciki.
Ta yaya ka gaya musu labarin?
Wannan shi ne mafi wahalar lamarin. To amma dole in gaya musu hakikanin abin da ya faru.
Dama kana da kusanci da su ne a baya?
A’a, ba ni da alaka da iyalinsa. Sai dai da  shi Abiola kansa. Na san dansa Kola. Na san likitansa Dokta Falomo, abokina ne. Koda a lokacin da ba ya da lafiya ne mukan yi hulda shi.
Amma iyalan, kamar matar, ka san yana da mata da yawa. Matar da ’yar ban san su ba. Sai na ce, “Ga abin da ya faru. Abu ne mai wahala. Ya kamu da rashin lafiya kuma ya rasu; kuma mun yi duk kokarin da za mu iya yi domin ceton ransa, amma ba mu samu nasara ba.”
Suka yi ta kuka da ihu, har daya daga cikinsu ta ce, “Sun kashe shi! Sun kashe shi!” Abu ne mai matukar tayar da hankali.