✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda 2023 ta tantance Okorocha bayan ya biya kotu belin N500m

Mai neman takarar shugaban kasa a Jam’iyar APC, Rochas Okorocha, ya bayyana a gaban kwamitin tantance ’yan takarar jam’iyar a daren ranar Talata. Okorocha dai…

Mai neman takarar shugaban kasa a Jam’iyar APC, Rochas Okorocha, ya bayyana a gaban kwamitin tantance ’yan takarar jam’iyar a daren ranar Talata.

Okorocha dai ya shiga hannun EFCC ne bisa zargin almundahana ta Naira biliyan 2.9.

Sai dai babbar kotun tarayyar ta ba da shi belin shi ranar Talata kan Naira miliyan 500, da kuma mai tsaya masa da zai ajiye Naira miliyan 500.

Yiwuwar Okorocha ya bayyana gaban kwamitin dai ya dade yana tada kura a fagen siyasar Najeriya kasancewar yana hannun EFCC.

Mai Shari’a Inyang Ekwo ya ba da belin Rochas ne bayan watsi da rashin amincewar hukumar EFFC kan hakan, inda ta ce kotun ta ajiye shi a hannunta domin zai iya tserewa.

Lauyan EFCC ya ce bayan keta dokar beli, Okorocha ya toshe duk wata kafa da hukumar za ta iya tuntubar sa, wanda hakan ne ma ya sa ta tsare shi bayan samun kamo shi.

Haka zalika lauyan EFCC ya ce tsohon gwamnan da ake tuhuma da laifuka 17 na almundaha, na da karfin ikon kawo matsala ga shaidun da suka tanada.

To sai dai lauyan Okorocha, Solomon Umoh ya tabbatar wa kotun cewa wanda yake karewa zai ci gaba da halartar zaman kotun, domin a cewarsa kasancewarsa dan kasa mai hankali, kuma dan takarar shugabancin kasa, ba zai taba aikata abin da zai zamo raini ga kotu ba.

A karshe dai Okorocha ya halarci tantancewar, kuma daga kansa ne kwamitin tantance ’yan takarar shugaban kasar jam’iyar ya kammala tantance su.

Masu neman takarar shugaban kasa a APC

Sauran masu neman takarar shugaban kasar da aka tantance sun hada da Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo; uban jam’iyyar APC na Kasa, Bola Tinubu; tsohon Ministan Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio; Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello; Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan.

Sai kuma tsohon Shugaban Majalisar Tarayya, Dimeji Bonkole; tsoho Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; da Tein Jack, da sauransu.

A ranar Litinin kadai Kwamitin ya tantance ’yan takara 12, ciki har da Pasto Tunde Bakare da Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru da tsohon gwamnan Ogun, Santa Ibikunle Amosun da tsohon gwamnan Zamfara Sani Yarima.

Kazalika akwai tsohon Ministan Ilimi, Chukwuemeka Nwajiuba da Pasto Felix Nicholas, da kuma kallabi tsakanin rawuna Misis Unu Ken Ohanenye, da kuma Sanata Ajayi, da dai sauransu.

Jam’iyar APC dai za ta gudanar da zaben fid-da gwaninta ranar 6 zuwa 8 ga watan Yuni a dadanlin Eagle Square da ke Abuja.