Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce wajibi Berlin ta kara wa Ukraine makamai don kare kanta daga barazanar dakarun Moscow.
Gidan Rediyon Jamus ne DW ya ruwaito Scholz yana bayyana hakan ne yayin da yake jaddada matsayar gwamnatinsa na hana Rasha cimma burinta na mamaye Ukraine.
- ’Yan matan FGC Yauri 11 na hannun ’yan bindiga bayan watanni 10 da sace su
- NAJERIYA A YAU: Hukuncin wanke bakin mai Azumi da rana
Olaf Scholz ya gayawa majalisar dokokin Jamus ta Bundestarg cewa, gwamnati na tattaunawar sirri da hukumomin Kyiv game da yiwuwar tabbatar da tsaro ga barazar da Moscow ke yi wa Ukraine
Gwamnatin Ukraine ta nemi agajin tsaro daga kasashen Turkiyya da China da Jamus, bayan da Rasha ta hana ta zama mamba a kungiyar hadakar tsaro ta NATO.
A makon nan ne Babban zauren Majalisar Dinkun Duniya ya kada kuri’ar dakatar da Rasha daga hukumar da ke kare hakkin dan Adam yayin wani zama da aka yi a birnin New York.
Matakin ya biyo bayan tuhumar da ake ma Rasha cewa sojojinta na aikata laifukan yaki a Ukraine.