Majalisar Dattawa ta ce ya zama tilas a yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari sakamakon jajircewarsa wajen inganta kasar nan ta hau tudun mun tsira duk da cewar akwai kalubale da ake fuskanta.
Shugaban Majalisar Sanata Ahmad Lawan ne, ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Gombe, yayin halartar taron tallafa wa jama’a da Sanata Sa’idu Ahmed Alkali, mai wakiltar mazabar Gombe ta Arewa ya shirya.
- Adadin wadanda suka mutu a guguwar Philippines ya haura 200
- Ka ziyarci jihohin da ake kashe-kashe —PDP ga Buhari
Ya ce shugaba Buhari, ya samar da shugabanci na gari da ci gaba ga kasar nan tun bayan karbar mulki da APC ta yi a shekarar 2015.
A kan haka ne Sanata Lawan ya ce sun sha alwashin ci gaba da goya wa Buhari baya don ganin ya cika alkawuran da ya daukar wa ’yan Najeriya.
Shugaban majalisar ya ce kada ‘yan Najeriya su bari a yaudare su a lokacin yakin neman zabe da cewar sake zabar APC na iya kawo rabuwar kai ga kasar nan da ma ‘yan kasar.