✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya yi aure sau 4 ya saki matar sau 3 cikin kwanaki 37

Wani mutumin kasar Taiwan da ya bullo da wani sabon wayo don a kara masa kudin hutu a wajen aiki, ya auri matarsa sau hudu…

Wani mutumin kasar Taiwan da ya bullo da wani sabon wayo don a kara masa kudin hutu a wajen aiki, ya auri matarsa sau hudu sannan ya sake ta sau uku duk a cikin kwanaki 37.

Dokar kasar Taiwan ta kayyade cewa, mutum na da ’yancin samun hutun kwanaki takwas sannan a biya shi kudin wannan hutu idan ya yi aure.

Hakan ya faru ga wani ma’aikaci mai mukamin magatakarda a wani bankin kasar, inda ya karbi kudinsa lokacin da ya yi aure a ranar 6 ga watan Afrilun bara.

Shi dai wannan ma’aikacin yana yin hakan don samun kudin na gaba bayan wadanda ya karba a baya.

A ranar karshensa na hutun kwanaki 8, sai mutumin ya saki matarsa da nufin ya sake aurenta washegarin ranar, kuma ya sake neman a biya shi wasu kudin hutun wanda yake ikirarin yana da ’yancin neman biyan shi wasu kudin kamar yadda dokar kasar ta tanadar.

Mutumin ya koma yana auren matar da suka rabu har sau hudu, sannan ya saketa sau uku duk a cikin kwanaki 37, wanda hakan ya sa yana da adadin kwanaki 32 da za a biya shi kudin hutun.

Shi dai wannan mutum ya kasance ya saki matarsa daya tilo, kuma bayan ya kammala hutunsa da kwana guda sai ya sake aurenta, bayan yin hakan sai mahukuntan bankin suka fahimci abin da yake shiryawa kuma suka hana shi daukar wani hutun da kudin hutun.

Hakan ya sanya mutumin ya shigar da korafi a cibiyar kwadago ta Taipei City Labor Bureau, yana kalubalantar bankin da cewa, sun saba dokar kasa saboda gaza kiyaye a rubutu mai lamba ta 2 na sashen dokar “Labor Leabe Rules”.

Ya bayyana cewa, ma’aikaci na da ’yancin a biya shi kudin hutun kwanaki 8 idan ya yi aure, tunda ma’aikacin ya yi aure sau 4, ya kamata a biya shi kudin kwanaki 32 na hutunsa.

Kungiyar ma’aikata ta Labor Bureau sun kaddamar da bincike kan magatakardar, inda kuma suka gano cewa bankin ya yi watsi da dokar kungiyar ma’aikatar.

A kan haka ake nemi bankin ya biya tarar dalar Amurka $20,000 daidai da Naira miliyan 7 da dubu dari shida, amma bankin ya daukaka kara kan ikirarin cewa, ma’aikacin ya saba ka’idar hutun auren saboda auren bogi ne cikin dokokin kwadago.