✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Ya ta kai karar mahaifinta ya yi mata ciki

Kotu ta sa a tsare shi a gidan yari bayan ya amsa laifinsa

Kotu ta tsare wani magidanci a kurkuku saboda zargin yi wa ’yarsa ciki.

’Yar mutumin ta shaida wa kotu cewa sau biyu uban nata yana mata fyade, kuma yanzu haka tana dauke da ciki wata hudu da ya yi mata.

Bayan an karanto masa tuhumar da ake masa, magidancin ya amsa cewa sau biyu yana zakke wa ’yar tasa watan Nuwamban shekarar, 2020 da kuma Janairun 2021.

Ya ce hakan ta faru ne a unguwar Asewele Korede Camp da ke unguwar Ore a Karamar Hukumar Odigbo, Jihar Ondo, amma yana rokon kotu ta yi masa afuwa.

Jami’in dan sandan mai gabatar da kara, Insifeto Jimoh Amuda, ya shaida wa kotun cewa Rundunar ’Yan Sandan Jihar ba ta kammala bincike kan lamarin ba.

Don haka ya bukaci kotun da ta dage sauraren karar don ba wa rundunar ’yan sanda damar ci gaba da fadada bincike kan lamarin.

A nan ne alkalin kotun, Mai Shari’a F.O. Omofolarin, ya bayar da umarnin ci gaba da tsare magidancin a gidan yari, sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Fabrairun 2021 don ba wa ’yan sanda damar kammala bincike.