✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya shiga hannu bayan tserewa da motar makarantar da yake aiki

Direban ya koka kan yadda makarantar ta rike masa albashin wata biyu.

Direban wata makarantar yara ya shiga hannun ’yan sanda bayan da ya tsere da motar makarantar.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Osun, CP Wale Olokode ne ya gabatar da wanda ake zargin a hedikwatar ’yan sandan a ranar Talata.

  1. An sanya ranar zaben shugaban kasa a Somaliya
  2. Ina nan daram a PDP — Mataimakin Matawalle

Olokode ya ce direban ya tsere da motar makarantar ‘Criterion Nursery and Primary School’ da ke garin Osogbo, inda aka dauke shi aiki watannin da suka gabata.

Kwamishinan ya ce wanda ake zargin ya tsere da motar zuwa yankin Ajah a Jihar Legas, sannan ya yi mata rajista da sunansa, ya fara haya da ita.

A cewar Olokode, wanda ake zargin ya amsa aikata laifin, don haka za a mika shi zuwa kotu don fuskantar shari’a.

Yayin zantawarsa da Aminiya, direban ya ce makarantar ce ta gaza biyan sa albashin wata biyu, alhali yana da mata da ’ya’ya biyar.

%d bloggers like this: