Wani mutum ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta na kasar Kuwait game da aure mafi karancin lokaci, inda ya ce “Aure ba tare da mutuntawa ba, na tun asali.”
Ya bayyana cewa wasu ma’aurata ne suka rabu bayan minti uku kacal da daura musu aure, bayan da angon ya zagi amarya da aikata ba daidai ba lokacin da suke fita daga wajen liyafar daurin auren, kamar yadda wani rahoto da jaridar Independent’s Indy ta wallafa.
Lokacin da aka kammala daurin auren kamar yadda aka saba, ma’auratan sun juya don ficewa daga cikin kotun da aka daura auren.
Sai dai wani ya yi kuskuren harɗe kafar amaryar ta faɗi.
A cewar wani rahoto a cikin jaridar Metro, angon ya zagi amaryar saboda faduwar da ta yi a gaban jama’a.
Jin haka sai amaryar ta fusata, ta buƙaci alƙalin da ya ɗaura auren ya soke auren nasu.
Alkalin ya amince kuma ya warware auen bayan minti uku kacal.
An ce auren shi ne mafi ƙarancin lokaci a tarihin kasar.
Lamarin wanda ya faru a shekarar 2019 yana sake yaduwa a shafukan sada zumunta.
“Na je wani biki inda ango yana jawabi yana yi wa matarsa ba’a kamar shi ya yi abin da mahaifinta ya yi, kamata ya yi ta yi abin da wannan matar ta yi,” wato ta ki tanka wa jawabin. Wani ya rubuta a shafin X (Twitter).
Wani kuma ya rubuta a dandalin sada zumunta na microblogging, “Aure ba tare da mutuntawa ba, tun ba a je ko’ina ba ya rushe.”
Wani ya kara da cewa: “Idan haka ne tun farko haka yake, zai fi kyau tun a farko ta bar shi.”
A shekarar 2004, wasu ma’aurata a Biritaniya sun shigar da kara suna neman raba aurensu bayan minti 90 da auren.
Fiye da sa’a daya bayan Scott McKie da Victoria Anderson sun yi musayar alkawura a Ofishin Rajista na Stockport a Greater Manchester, alakar aurensu ta yanke.
Matar ta fusata da gallazawar da mijinta ya yi wa kawayen amaren, inda ta kwada wa angon farantin zuba tokar sigari a lokacin liyafarsu.
A lokacin da aka kira ’yan sanda, ya bugi kan wani jami’i daya sannan ya bugi daya a fuska kafin a kai shi ya kwana a gidan yari yayin da matarsa ke neman saki ta hanyar soke hutun amarcin da suka yi na Corfu.