Wani mai satar mutane ya shiga hannu bayan da ya sace wasu masu gadin kamfani a kauyen Jeje Jijipe da ke Karamar Hukumar Karu Jihar Nasarawa.
Kakakin ’Yan Sandna Jihar, DSP Ramhan Nansel, ya ce, a ranar Asabar suka samu rahotan cewa wani mutum da ba a san ko wane ne ba, ya sace wasu masu gadin kamfanin hada ruwan leda su biyu.
“Da samun rahoton Kwamishinan ’yan sandan jihar, Maiyaki Mohammed-Baba, ya tashi rundunar ’yan sanda ta musamman karkashin jagorancin CSP Nnamdi Udobor, DPO na yankin domin farauto mutumin.
“Binciken ya kai ga bankado wani matashi mai shekaru 32 a Karamar Hukumar Tafa ta Jihar Kaduna da aka samu mutanen a hannunsa.
“Daga nan ya jagoranci ’yan sandan zuwa unguwar Hilltop, inda ya boye masu gadin,” in ji sanarwar da kakakin ya fitar a ranar Talata.
Ya ce an samu wata bindiga kirar gida da wanda ake zargin ya yi amfani da ita wajen aikata laifin, sannan an sada masu gadin da ya sace da iyalansu.
Yanzu haka dai bisa umarnin kwamishinan ’yan sandan, an mika wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuka domin gurfanar da shi gaban kotu.