✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ya nemi rabuwa da matarsa kan almubazzaranci

Ya kuma shaida wa kotun cewa matar na yawon gantali, ga rashin kula da yara, don haka, ya gaji da zama da ita.

Wani magidanci a Abuja ya bukaci kotu ta raba aurensu da matarsa saboda tana barnar abinci.

A kotun a ranar Alhamis, magidanci ya matarsa ba ta iya tattalin abubuwa a gida ba, don haka ya nemi kotun da ke zamanta a yankin Jikwoyi, ta kashe auren don ya jefar da kwallon mangoro ya huta da kuda.

“Ko kadan matata ba ta san cewa abubuwa suna wahalar samu a kasa ba.

“Idan ta tashi yin abinci, sai ta girka fiye da kima, karshe sai dai a zubar,” in ji shi.

Ya kuma shaida wa kotun cewa matar na yawon gantali, ga rashin kula da yara, don haka, ya gaji da zama da ita.

A cewarsa, munanan halayen da matarsa ke nuna masa sun sa ya kamu da lalurar hawan jini.

A nata bangaren, matar ta musanta zarge-zargen da maigidan nata ya yi mata.

Bayan sauraron duka bangarorin, alkalin kotun, Labaran Gusau, ya dage shari’ar zuwa ranar 17 ga Nuwamba.